Za Mu Doke Atletico Madrid Har Gida, Hansi Flick
Published: 1st, March 2025 GMT
Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Hansi Flick, ya bayyana cewa kungiyarsa za ta je har gidan Atletico Madrid ta doke ta a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin Coppa Del Rey, bayan da Barcelona da Atletico Madrid suka tashi 4-4 a wasan farko zagayen daf da karshe a Copa del Rey ranar Talata a filin wasa na Estadi Olimpic Lluis Companys.
Minti daya da fara wasan Atletico Madrid ta fara cin kwallo ta hannun Julian Albarez, sannan Griezmann ya kara ta biyu a minti na biyar Tsakani amma daga baya Barcelona ta zare daya ta hannun Pedri a minti na 19, sannan Cubarsi ya farke ta biyu minti uku Tsakani sannan kafin hutu Barcelona ta kara ta uku ta hannun Martinez, haka suka je zagayen farko Barcelona na cin 3-2.
Noman Dabino: Jigawa Ta Yi Hadaka Da Saudiyya Yawan ’Yan Kasashen Waje Da Suka Shigo Kasar Sin Ba Tare Da Biza Ba A Bara Ya NinkuBayan da suka koma zagaye na biyu ne, sai Barcelona ta ci ta hudu a karawar ta hannun Lewandowski kai kace an tashi da Atletico Madrid a wasan amma daga baya kungiyar da Diego Simeone ke jan ragama ta zare kwallo ta uku ta hannun Llorente daga baya ta zare ta hudu ta hannun Sørloth dab da za a tashi daga wasan wanda yaja hankalin ‘yan kallo a duniya.
Wannan shi ne karo na biyu da suka kece raini a tsakaninsu a bana, bayan da Atletico ta je ta doke Barcelona a La Liga ranar 21 ga watan Disamba kuma a ranar Laraba 4 ga watan Afirilu, Atletico za ta karbi bakuncin wasa na biyu a daf da karshe a Copa del Rey. Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 54, iri daya da na Real Madrid ta biyu da kuma Atletico mai maki 53 ta ukun teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Barcelona
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi
Nijar ta fice daga rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Tafkin Chadi da ke yammacin Afirka yayin da take ƙoƙarin inganta tsaro kan albarkatun mai a cikin gida.
A shekarar 2015 ce Nijeriya da Chadi da Kamaru da Nijar suka sake farfaɗo da rundunar haɗin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF), wacce aka ƙirƙira a shekarar 1994 don yaƙi da ƙungiyoyin jihadi a kewayen Tafkin Chadi.
NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana Azumin Sitta Shawwal a MusulunciSai dai har yanzu ana ci gaba samun rarrabuwar kai da matsalar rashin daidaito na hana rundunar samun nasara sosai, lamarin da ya sa ƙungiyoyin ‘yan bindiga a yankin cin karensu ba babbaka.
Kamfanin Dillancin Labaran Reuters da ya ruwaito sanarwar gwamnatin ƙasar Nijar ɗin ya ce kawo yanzu MNJTF ba ta yi tsokaci game da ficewar Nijar ɗin ba, yana mai ƙarawa da cewa babu tabbas game da yadda matakin zai yi tasiri kan aikin rundunar a nan gaba.
Yankin Tafkin Chadi yana fama da hare-haren ‘yan bindiga ciki har da ‘yan kungiyar ISWAP da Boko Haram, waɗanda suka ƙaddamar da yaƙi a arewa maso gabashin Nijeriya a shekarar 2009 kuma sun kashe dubban mutane.
A bara, Chadi ta yi barazanar ficewa daga MNJTF bayan an kashe sojojinta kusan 40 a wani harin da aka kai wani sansanin soji.
Nijar tana rage hulɗa da wasu maƙwabtanta tun bayan da sojoji suka hamɓarar da gwamantin Shugaba Mohamed Bazoum a shekarar 2023. Tare da Burkina Faso da Mali – ƙasashe maƙwabta, inda sojoji suka karɓe kwanan nan – ta janye daga ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) a shekarar 2024.
Sojojin da ke mulki a Nijar, da suka yi shelar tsarin miƙa mulki na shekara biyar, sun yi alƙawarin tabbatar da tsaro a ƙasar, wadda ‘yan ci-rani da masu safarar mutane ke ƙetarewa ta cikin gagarumar hamadar arewacinta.