HausaTv:
2025-04-02@20:21:25 GMT

Motocin Buldoza Suna Ta Rusa Gidajen Falasdinawa A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Published: 2nd, March 2025 GMT

Kungiyar Hamas ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a yankin yamma da Kogin Jordan tana rusa gidajen Falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nur- Ashamsh, a ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Nihad Ashawish shugaban kwamitin mai kula da sansanin yan gudun hijirar yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa a jiya Asabar ce motocin Buldoza na HKI suka shiga unguwar Almanshiya suka rusa gidajen wasu Falasdinawa, sannan suka bata hanyoyi a unguwar.

Kamfanin dillancin labaran Abadulu na kasar Turkiya ya nakalti Ashawish yana cewa, sojojin HKI su kan tilastawa Falasdinawa fita daga gidajensu sannan su rusasu a gabansu. Tare da umurnin su fice daga yankin su je inda suka ga dama.

Hamas ta kammala da cewa da wannan aikin zamu fahinci cewa gwamnatin HKI tana son kara korar Falasdinawa daga kasarsu, musamman daga yankin yamma da kogin Jordan.

Kungiyar ta bukaci MDD ta dauki matakan da suka dace don hana yahudawan mamayar karin gidajen Falasdinawa a arewacin yankin yamma da Kogin Jordan.

A jiya Asabar kwanaki 21 cur Kenan gwamnatin HKI take rurrusa gidaje da lalata hanyoyi a garuwan Falasdinawa dake yankin yamma da kogin Jordan musamman garuruwan Tulkaram, da Jenin.

Majiyar asbitoci a yankin yamma da kogon Jordan sun bayyana cewa daga lokacin zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 64 sannan wasu dubbai an koresu daga gidajensu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a yankin yamma da

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Nijar, ta saki ministocin hambarariyar gwamnatin Bazoum

Gwamnatin Nijar ta saki kusan mutane 50 da suka hada da ministocin da aka tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.

Baya ga tsaffin ministocin da akwai wasu sojoji da ake zarginsu da yunkurin juyin mulki a shekarar 2010 da suma aka sake su.

 “An sako wadannan mutane ne bisa ga shawarwarin da babban taro na kasar ya bayar,” kamar yadda sakataren gwamnatin kasar ya karanta a gidan talabijin din kasar a cikin daren jiya.

Cikin tsaffin ministocin da aka saki har da tsohon ministan man fetur Mahamane Sani Issoufou, dan tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou, da kuma tsohon ministan tsaro Kalla Moutari, da tsohon ministan kudi Ahmat Jidoud, da kuma tsohon ministan makamashi Ibrahim Yacoubou.

An kuma saki sojojin da a baya aka samu da laifin yunkurin juyin mulki da kuma janyo “barazana ga tsaron kasar”, ciki har da Janar Salou Souleymane, da tsohon babban hafsan hafsoshin sojin kasar, da wasu jami’ai uku da aka yankewa hukuncin daurin shekaru 15 a shekarar 2018 a gidan yari, saboda kokarin hambarar da Shugaba Issoufou a shekarar 2015.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato
  • Isra’ila na karbe yankuna a zirin Gaza
  • Gwamnatin Nijar, ta saki ministocin hambarariyar gwamnatin Bazoum
  • Mamakon Ruwan Sama: Matafiya sun Maƙale a Taraba Sakamakon Ɓallewar Gada
  • Kasar Sin Za Ta Yi Ramuwar Gayya Kan Takunkumin Biza Da Amurka Ta Kakaba Wa Jami’anta
  • Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCL
  • Nijar Ta Fice Daga Rundunar Tsaro Ta Haɗin Kai MNJTF
  • Sin Ta Gano Babban Yankin Hakar Danyen Mai A Tekun Kudancin Kasar
  • Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Kasashen Yamma Sune Yan Ta’adda Na Gasliya A Yankin