Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kashe akalla yara 16 tun farkon wannan shekara ta 2025 a yankin yamma da kogin Jordan.

Tashar talabijin ta Presstv  a nan Tehran ta nakalto Ayed Abu Eqtaish, daraktan kungiyar ‘ The Defense for Children International’ a yankin yamma da kogin Jordan yana fadar haka.

Ya kuma zargi manya manyan kasashen duniya da kyale gwamnatin HKI tana aikata irin wadannan laifuka kan Falasdinawa a gaban idan kowa.

Eqtaish ya kara da cewa, rashin magana da kuma takawa gwamnatin yahudawan birki yana sa ta kara yawan kashe yara Falasdinawa a duk sanda ta ga dama.

Kafin haka wani rahoton MDDya bayyana cewa idan ba’a hana HKI da karfi ba, to ba za ta takaita kisan kiyanshi a Gaza kadai ba, zata fadadashi zuwa yankin yamma da kogin Jordan.

Sojojin HKI sun ta aikata kissan kiyashi a gaza a yain fin karfin da ta yi a Gaza na tsawon watanni 15, inda ta kashe fal;asdinawa fiye da 61,000 kafin a tsagaita wuta a ranar 19 ga watan Jenerun da ya gabata.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Taron Kara Wa Juna Sani Kan Canton Fair Ya Ja Hankalin Masu Masana’antu Da ‘Yan Kasuwan Habasha

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar NOA Ta Bukaci Al’umma Su Kara Hakuri Da Kaunar Juna
  • Hamas: Matakin Netanyahu na hana shigar kayan agaji a Gaza keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne
  • Yan Ta’adda Sun kashe Sojojin Sa Kai Na Basij Biyu A Yankin Kudu Maso Gabacin Kasar Iran
  • Motocin Buldoza Suna Ta Rusa Gidajen Falasdinawa A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
  • Kasar Masar Ta Tabbatrawa Falasdinawa, Tana Bayansu Kafin Taron Kasashe Larabawa
  • A Yau Ce Dokar Haramta Amfani Da Tankunan Mai Masu Daukar Lita 60,000 A Najeriya
  • Taron Kara Wa Juna Sani Kan Canton Fair Ya Ja Hankalin Masu Masana’antu Da ‘Yan Kasuwan Habasha
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Masallacin Juma’a A Garin Samamiya Da Ke Birnin Kudu
  • Yawan ’Yan Kasashen Waje Da Suka Shigo Kasar Sin Ba Tare Da Biza Ba A Bara Ya Ninku