A wani bidiyo mai ban mamaki da Hukumar Kashe Gobara ta yankin Tulsa da ke kasar Amurka ta fitar ya nuna yadda wani kare ya yi sanadin tashin wuta a wani gida ta hanyar tauna fakitin batirin Lithium.
Hukuma ta kama karen bayan gano hakan a bidiyon mai ban mamaki, wanda ya nuna shi yana tauna fakitin batirin lithium-ion wanda mai shi ya bari.
Bayan dan lokaci da fara taunawa, baturin ya fara tarwatsin wuta, sannan ya yi bindiga, lamarin da ya sa karen da wata kyanwa da ke kwana a kusa da gidan tserewa don tsira da rayukansu.
An yi sa’a, duk dabbobin sun tsere ta kofar gidan, wutar ba ta yi musu lahani ba, amma gobarar ta yi mummunar barna a gidan.
Masu kashe gobara a yanzu suna amfani da bidiyon a matsayin gargaɗi game da barin batir lithium a wurin da yara da dabbobi za su iya kaiwa.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Kashe Gobara ta Tulsa ya ce, duk da irin barnar da gobarar ta yi, abubuwa na iya zama mafi muni idan akwai mutane da ke kwana a ciki, ko kuma yadda za a iya tsira da dabbobi marasa galihu.
“Lokacin da wannan wutar batirin ta fara ba tare da katsewa ba, ta haifar da zafi da samar da iskar gas mai konewa da guba har ma da tartsatsi,” in ji daya daga cikin ma’aikatar kashe gobaran, Andy Little game da makamashin da yake cikin kananan baturan lithium.
Ya ce, “Yana da mahimmanci ku bi ka’idojin masana’anta lokacin amfani da baturan lithium-ion, kawai amfani da caja da aka yarda da su da adana su a wajen da yara da dabbobin gida.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Zata Gudanar Da Tarin Kare Hakkin Bil’adama Ta Faskar Gabacin Duniya A Karo Na Farko
Shugaban hukumar al-adun musulunci da sadarwa a nan Iran Mohammad Mehdi Imamipour ya bayyana cewa za’a gudanar da taron kasa da kasa na kare hakkin bil’adama a karon farko a nan kasar Iran tare da mahangar kasashen gabas.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Imanipour yana fadar haka a yau, ya kuma kara da cewa za’a bude tarurrukan ne a nan birnin Tehran, Qom da kuma Esfahan a lokaci guda daga ranar 28 ga watan Afrilu zuwa 2 ga watan mayu.
Labarin ya ce matsalar kare hakkin bil’adama yana daga cikin al-amuran da ake nuna faska biyu a cikin al-amura da dama a duniya, musamman kan abinda yake faruwa a kasar. Imanipour y ace suna son gudanar da taron ko wani shekaru 4.
Ya zuwa yanzu dai inji shi, an gayyaci masana da kwararru daga kasashe 32 a duniya. Sannan an karbi rubuce-rubuce har 491, daga ciki 186 daga Amurka, Austria, Masart, Kenya, Tunisia, Rasha, China, Kazakhstan, Indonesia, Lebanon, Malaysia, Iraq, Nigeria, Serbia, Espaniya da kuma Netherlands. Har’ila yau tare da 305 daga cikin gida.
Daga karshe yace JMI tana son a samarda wata sabuwar mahanga ta kare hakkin bil’ada a duniya sabanin wadanda kasashen yamma suke jagoranta a halin yanzu.