Shugaban Kasar Ukraine Ya Sami Tarba Mai Kyau A Burtaniya Bayan Cacan Baki Mai Zafi Da Trump
Published: 2nd, March 2025 GMT
Shugaban kasar Ukrain Volodomyr Zelesky ya samu tarba mai kyau a kasar Burtaniya bayan ya isa birnin London a jiya Asabar kuma bayan cacan baki mai zafi da yayi da shugaban Amurka Donal Trump a fadar White House dangane da yakin Ukraine.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa shugaba Zeleski ya gana da firaiministan kasar Burtania Keir Starmer, wanda ya yaba masa kan yadda ya tsayawa kasarsa da kuma kasashen turai a gaban shugaban Amurka Donal Trump da mataimakinsa a ranar jumma’an da ta gabata.
Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya zanta da shuwagabannin biyu, wato Trump da kuma Zeleski don kwantar da hankali.
A yau Lahadi ce za’a gudanar da taro na musamman kan abinda ya faru tsakanin Zelesky da Trump da kuma makoman kasar Ukraine a yakin da take fafatawa da Rasha tun shekaru 3 da suka gabata.
Sauran shuwagabannin kasashen Turai sun yabawa Zelesky da yadda ya tsayawa kasarsa da kasa kasashen turai a tattaunawarsa mai zafi da manya-manyan Jami’an gwamnatin Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta yi watsi da tattaunawa kai tsaye dangane da shirinta na makamashin Nukliya, sannan ya kara da cewa amma tattaunawa tare da masu shiga tsakani a bude take.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana cewa tuni, mun bawa gwamnatin Amurka amsar wasikar da ta aiko mana, inda a cikinta, muka kara jaddada cewa babu wata tattaunawa kai tsaye da Amurka, kuma an tura wasikar ta inda na Amurkan ta fito wato ta kasar Omman. Don haka muna jiran matakan da Amurka zata dauka a kan amsar.
Daga karshe shugaban ya kammala da cewa duk wata mu’amala da gwamnatin kasar Amurka ba zai taba yiyuwa kai tsaye ba, wannan kuma saboda mummunan tarihin da Amurkawa suke da shin a karya al-kawali a duk wata yarjeniyar da aka cimma da ita a baya.
Ya dukkan tarihin JMI bata taba sabawa alkawalin da ta dauka da wata kasa ba, amma gwamnatin Amurka kuma tana da mummunan tarihi na sabawa alkawali don haka a halin yanzu ya rage mata ta sauya halayenta.