Abubuwan da ya kamata a sani game da azumin watan Ramadana
Published: 2nd, March 2025 GMT
Bismillahir Rahmanir Rahim Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya isar da komai.
Tsira da amincin Allah su tabbata bisa ga Annabi (S.A.W) da kuma bayinsa zababbu.
Bayan haka. Wannan wani dan takaitaccen sako ne nake so na isar da shi ga ’yan uwa Musulmi, na ciro hujjojinta daga littafin Allah (S.
Sai na ambaci sunan littafin: “RAMADANIYYA” Ina ba da kyauta ga kowane Musulmi da Musulma wato mai Azumi, maza da mata.
Ina rokon Allah Ya sanya shi a cikin mizanin kyawawan ayyukanmu a ranar saduwa da Shi da Aljannar ni’ima. Allah Ya sa haka.
Ina rokon duk wanda ya ga wadansu kurakurai ya aikomin don nan gaba in gyara su. .
1. Ayoyi da suka yi magana a kan azumi
Da sunan Allah, mai Rahma, mai Jinkai. Allah Ya ce a cikin Al-Kur’ani Mai Girma: “Ya ku wadanda ku ka yi imani! An wajabta Azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan mutanen da ke gabaninku, tsammanin za ku ji tsoron Allah” (183).
Kwanuka kidayayu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuma yana a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala akwai fansa, ciyar da matalauci, sai dai wanda ya kara alheri, to shi ne mafi alheri a gare shi. Kuma ku yi Azumi (da wahalar) ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani (184).
Shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rabewa. To, wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa akan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam. Allah Yana nufin sauki a gare ku, kuma baya nufin tsanani gare ku, kuma domin ku cika adadin, kuma domin ku girmama Allah a kan Ya shiryar da ku, kuma tsammanin ku, zaku gode (185).
Kuma idan bayiNa suka tambaye ka daga gare ni, to lalle Ni Makusanci ne. Ina karbar kiran mai kira idan ya kira Ni. Saboda haka su nemi karbawaTa, kuma su yi imani da Ni, tsammaninsu, su shiryu (186).
An halatta a gareku a daren Azumi, yin jima’i zuwa ga matanku, su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su, Allah Ya sani, lallai ne ku, kun kasance kuna yaudarar kanku. Saboda haka Ya karbi tubarku, kuma Ya yafe muku. To, yanzu ku rungume su, kuma ku nemi abinda Allah Ya rubuta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baki daga alfijir, sa’an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhali, kuna masu itikafi a cikin masallatai. Wadancan iyakokin Allah ne, don haka kada ku ketare su, kamar haka ne Allah Yake bayyana ayoyinSa ga mutane tsammaninsu, za su yi takawa. (187).
Kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da karya, kuma ku sadar da ita zuwa ga mahukunta domin ku ci wani yanki daga dukiyoyin mutane da zunubi, alhali kuwa ku, kuna sani. (188) Suratu Bakara.
2. Hikimar wajabta yin azumi
Mu fara da sunan azumi wato “Ramadan”. Ramadan suna ne na watan tara daga watannin Musulunci, shi ne kuma watan da Allah Ya ambace shi karara.
Hikimar da ta sa aka wajabta mana azumi don tsarkake rai ne da kuma sa mata tsoron Allah don ta samu dacewa a gobe Lahira.
3. Ladubba wajibabbu ga mai azumi
1. Wajibi ne ga mai Azumi ya tashi da niyyar cewa azumi ibada ne cikin maganganunsa da aikace-aikacensa.
2. Ya nisanci abubuwan da aka haramta kuma ya tsare ganinsa da jinsa da tafiyarsa daga haramtattun abubuwa. Wadannan wajibi ne ga mai azumi ya kiyaye su idan yana so azuminsa ya karbu a wajen Allah.
4. Abubuwan da ake so ga mai azumi
1. Jinkirta yin sahur.
2. Gaggauta yin buda baki.
3. Yawan karatun Al-Kur’ani mai Girma.
4. Yawaita adu’oi na alheri.
5. Yawaita sadaka.
6. Yawan ambaton Allah da tsarkake Shi da sauran ayyukan alheri.
5. Falalar watan ramadan
1. A cikinsa aka saukar da Al-Kur’ani: Allah Yac e: ‘Watan Ramadan ne aka saukar da Al-Kur’ani a cikinsa.”
2. Ana gafarta zunubi a cikinsa: Annabi tsira da amindn Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Wanda ya yi azumin watan Ramadan yana mal imani yana mai neman lada, to an gafarta masa abin da ya gabata na laifufukansa” Imamu Bukhari ne ya ruwaito hadisin.
3. Amsar adu’ar mai Azumi: Annabi (SAW) yace: “Ana karbar addu’ar mutane uku, mai azumi lokacin bude baki, da shugaba mai adalci da wanda aka zalunta”.
4. Daran Lailatul-Kadiri: Allah Ya ce: “Daren Lailatul-kadiri ya fi wata dubu wajen alheri.”
5. Ana daure shaiddanu: Annabi (S.A.W) ya ce “Idan Ramadan ya zo ana daure shaidanu kuma a bude kofofin Aljanna”.
6. Yin Umra a watan Ramadan yana daidai da aikin Hajji.
6. Ma’anar azumi
Abinda ake nufi da azumi “kamewa da barin ci da sha da saduwa da iyali da duk wani abu da zai shiga cikin ciki daga fitowar alfijiri har zuwa faduwar rana. Yin haka daya ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar.
Don haka ne wajibi ne akan Musulmi da Musulma baligai masu hankali kuma da lafiya da za su iya yin Azumi su yi.
Daga CSP Imam Ahmad Adam Kutubi da Muka’ila Usman BT Imam Nigerian Police Force, Zone 7, Police Headkuarter, Abuja
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ramadan watan Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya
Hukumomi a Ƙasar Saudiyya, sun tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin yau Juma’a.
Hakan na nuni da cewa azumin bana zai fara a ranar Asabar, 1 ga watan Maris, 2025.
Shafin Haramain Sharifain ne, ya tabbatar da wannan sanarwa, yayin da aka ga jinjirin watan a wurare daban-daban na ƙasar.
Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan KanoWannan na nufin cewa Musulmai a Saudiyya za su fara azumi a ranar Asabar.
Hakazalika, ƙasashen Qatar da Oman sun sanar da cewa za su fara azumin Ramadan a wannan ranar Asabar.
A yayin da ake shirin shiga wannan wata mai alfarma, an yi kira ga Musulmai da su yi amfani da lokacin azumi wajen ƙara yawan ibada, yin kyawawan ayyuka, da taimaka wa marasa galihu, duba da yanayin tattalin arziƙin duniya.
Ana sa ran cewa, Saudiyya da wasu ƙasashe, za a fara azumin Ramadan a sassa daban-daban na duniya a ranar Asabar, 1 ga watan Maris, 2025.