Hamas: Matakin Netenyahu Na Dakatar Da Shigar Kayan Agaji Cikin Gaza Keta Yarjejeniya Ne
Published: 2nd, March 2025 GMT
Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani na kasa da kasa da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya su dakatar da azabatar da fiye da mutane miliyan daya da suke yi ta hanyar hana shigar da kayan agaji.
Kungiyar ta Hamas wacce ta fitar da sanarwa a yau Lahadi ta ce, matakin da Netanyahu ya dauka na dakatar shigar da kayan agaji cikin Gaza, wata tsokana ce, kuma laifin yaki ne sannan uwa uba keta yarjejeniyar datakar da wuta da musayar fursunoni ce.
Bugu da kari, kungiyar ta Hamas ta ce bukatar da Netanyahu ya gabatar na tsawaita zango na farko na yarjejeniyar, wani yunkuri ne na gujewa aiwatar da ita kanta yarjejeniyar.
Haka nan kuma Hamas ta bukaci Amurka da ta daina zama mai goyon bayan manufofin Netanyahu, tana mai jaddada cewa duk wani kokari na take hakkokin Falasdinawa ba zai haifar da da, mai ido ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Manufar Kasarsa Da Shirin Kare Muradunta A Duk Wata Yarjejeniya
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da ci gaba a kan tafarkinta. Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Babu kyakykyawan fata kuma ba za a fitar da rai ba.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da yake jawabi a taron da gwamnonin kasar suka yi a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar a yau, ya yi jawabi kan shirin tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai cewa: Tun da fari gwamnatin Iran ta jaddada cewa tana kokarin karfafa dangantakar siyasa da tattalin arziki da kimiyya da al’adu da sauran kasashe, musamman ma kasashen musulmi da na makwafta. Iran tana kuma neman kyakkyawar mu’amala da sauran kasashe bisa mutunta juna.