HausaTv:
2025-03-03@09:29:36 GMT

Nijar: An Kashe Sojoji 11 A Wani Hari Na Kungiyar al-Ka’ida

Published: 2nd, March 2025 GMT

Rahotanni da suke fitowa daga Nijar sun bayyana cewa; Wata kungiyar mai alaka da al-ka’ida ta  dauki alhakin kashe sojojin kasar 11 a kan iyaka da Aljeriya.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai lamarin ya faru,kuma a jiya Asabar ne aka yi jana’izarsu a garin Agadez, kamar yadda wata majiyar watsa labara ta jamhuriyar Nijar ta ambata.

Shafin “Air Info” da ya watsa laabrin ya kuma ce; Jami’an soja da dama sun hjalarci jana’izar sojojin da su ka kwanta dama, daga cikinsu har da janar Musa Salih Barmo, babban hafsan hafsoshin sojan kasar.

Tashar Radiyo din kasar ta Nijar ta ce, an yi wa sojojin kwanton bauna ne a lokacin da suke sintiri akan  mahadar iyakaokin kasar, da Mali da kuma Burkina Faso.

Labarin Radiyon ya kuma ce, Janar Barmo ya nufi asibitin garin Agadez din domin yin dubiyar sojojin da su ka jikkata.”

 A gefe daya wata kungiyar mai  suna; “Nasratul-Islam Wal Muslimin” da reshe ne na alka’ida, ta dauki alhakin kai harin.

A lokuta da dama a baya sojojin na jamhuriyar Nijar sun sha fuskantar hare-hare irin wadannan, sai dai ba kasafai kungiyoyin da suke ikirarin jihadi suke daukar alhakin kai wa ba.

Saharar dake Arewacin Nijar tana da girma kuma tana kusa da kasar Libya da masu hada-hadar mutane da kuma  ‘yan hijira suke bi suna ratsawa domin shiga cikin kasashen turai.

Kungiyar “Ikilid” wacce ba ta gwamnati ba da take sa ido akan duk wasu rikice-rikice da suke faruwa a duniya, ta ce daga 2023 zuwa yanzu an kashe mutane 2400 a cikin wannan kasa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara

Dakarun Sojin ‘Operation FANSAN YANMA’, sun kama Ƙasurgumin Shugaban ’Yan Bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu, wanda ya addabi al’ummar Mada, Tsafe, da wasu yankunan Jihar Zamfara.

Dakarun sun kai farmaki Hegin Mahe, Ruwan Bore, garin Mada, a Ƙaramar Hukumar Gusau a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Cibiyar bincike ta nemi a tabbatar da dokar kare haƙƙin mata a Arewa Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano

Bayan musayar wuta, sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga, yayin da Nabamamu ya tsere zuwa cikin wani gida, amma daga ƙarshe dakarun suka cafke shi.

Bayan kama shi, ɗaya daga cikin yaransa, Bakin Malam, ya jagoranci kai harin ramuwar gayya wasu ƙauyuka, wanda ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa.

Sai dai dakarun sun mayar da martani, inda suka fatattaki ’yan bindigar, tare da ƙara jibge sojoji don tabbatar da tsaro a yankin.

Nabamamu, ya kasance almajiri ne, daga baya ya zama hatsabibin ɗan bindiga wanda ya yi sanadin ajalin mutane masu yawan gaske.

Ya jagoranci sama da mayaƙa 100, inda yake karɓar haraji daga hannun mazauna wasu ƙauyuka, kuma yana da alaƙa da masu yi wa wasu mahara safarar makamai a yankin.

Kama shi na iya rage ƙarfin ’yan bindiga a Zamfara, yayin da sojoji ke ƙara ƙaimi domin kawar da barazanar tsaro da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yan Ta’adda Sun kashe Sojojin Sa Kai Na Basij Biyu A Yankin Kudu Maso Gabacin Kasar Iran
  • Al-Houthi : Isra’ila Na fakewa Da Goyan Bayan Amurka Tana Karya Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza
  • Haleyen Kirki 14 Da Ake Bukata Daga Malamin Makaranta (1)
  • Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta ‘Euro-Med Monitor’ Ta Ce Ta Sami Shaidu Wadanda Suka Tabbatar Da Cewa HKI Tana Azabtar Da Fulasdinwa
  • An Yi Jana’izar Shahidan kungiyar Hizbullah Fiye Da 120 Kudancin Kasar Lebanon A Yau Jumma’a
  • Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Nabamamu a Zamfara
  • Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara
  • An kori ma’aikatan Microsoft saboda adawa da yahudawan sahyoniya
  • Kasashen Habasha da Nijar sun tattauna kan inganta hadin gwiwar soji da tsaro