Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi
Published: 2nd, March 2025 GMT
’Yan sanda sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki.
Bayanai sun ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi.
Burina in yi fice kamar mahaifiyata — Maryam ‘Yar Auta Abubuwan da ya kamata a sani game da azumin watan RamadanaKakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya ce, “saɓani ne ya kaure tsakanin wani mai suna Nuru Isah mai shekara 50 da matarsa ta biyu, Wasila Abdullahi kan tsarin abinci da kayan buɗa-baki na gidan.
’Yan sanda sun ce bincike farko na nuna cewa mijin ya yi amfani da bulala wajen bugun matar mai shekaru 24, “inda ta yanke jiki ta faɗi, da aka kai ta asibitin koyarwa na jami’ar Tafawa Ɓalewa ne likitoci suka tabbatar da rasuwarta.”
Sanarwar ta ƙara da cewa ’yan sanda sun kama mijin, sun ɗauko bulalar da aka yi amfani da ita, sannan kuma za a yi binciken ƙwaƙwaf a kan gawar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Musa Muhammad, ya bayyana cewa za a gudanar da bincike domin tabbatar da adalci a lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Azumin Ramadan Jihar Bauchi
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin Dakatar Da Shugaban Ma’aikatan jihar Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da Muƙaddashin Shugaban Ma’aikata kuma babban Sakatare na sashin shirye-shirye, Salisu Mustapha, bisa zargin yin kutse a albashin ma’aikatan gwamnati da rashin biyan wasu daga cikinsu.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar daren Alhamis, an bayyana cewa dakatarwar ta fara aiki nan take, tare da umartar Mustapha da ya sauka daga matsayin babban Sakatare don bai wa kwamitin bincike damar gudanar da aikinsa ba tare da katsalandan ba.
Labarin Bukar, Malamin Da Ya Shafe Watanni 20 Ba Tare Da Albashi Ba A Borno Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Zaftare Albashin Ma’aikataA don ci gaba da gudanar da harkokin ofishin, gwamnan ya nada Malam Umar Muhammad Jalo, Babban Sakatare na bincike, kimantawa da tsare-tsare (REPA), a matsayin sabon muƙaddashin shugaban ma’aikata har sai an kammala bincike.
Wannan matakin na zuwa ne bayan kafa kwamitin mutum bakwai ƙarƙashin Hon. Abdulkadir Abdussalam da ke da wa’adin kwanaki bakwai don gano gaskiyar lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp