Sakon Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya Na Murna Fara Azumin Ramadan
Published: 2nd, March 2025 GMT
Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci.
A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga kowa.
Ina taya mu murnar zuwan watan Ramadan mai alfarma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — Jamus
Gwamnatin Jamus ta ce tana ci gaba da samun galaba na daƙile kwararar baƙin haure masu shiga ƙasar tare da mayar da wadanda aka yi watsi da takardunsu na neman mafaka zuwa inda suka fito.
Ministar harkokin cikin gida ta Jamus, Nancy Faeser, ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar mai barin gado ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile shigar baƙin haure cikin ƙasar.
Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu FarautaFaeser ta ce gwamnatin na ci gaba da daukan matakin mayar da baƙin haure ƙasashen da suka fito, inda yanzu haka aka samu raguwar masu ajiye takardun neman mafaka a ƙasar, mafi ƙarfin tattalin arziki tsakanin ƙasashen Turai.
Faeser ta ce gwamnatin da Olaf Scholz ke jagoranta ta aiwatar da manufofi masu tasiri da suka taimaka wajen daƙile shigar baƙin haure zuwa ƙasar Jamus.
Nancy Faeser ’yar jam’iyyar SPD mai mulki za ta ajiye muƙamin na ministar cikin gida da zarar an kafa sabuwar gwamnati, bayan zaɓen da jam’iyyar CDU ta kasance a matsayi na farko wanda aka yi ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekara ta 2025.
Ana sa ran Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama shugaban gwamnatin na gaba da za a kafa a ƙasar ta Jamus.