Aminiya:
2025-03-03@09:39:06 GMT

Sojoji sun ƙwato makamai a dajin Sambisa

Published: 2nd, March 2025 GMT

Dakarun Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar JTF na Operation Hadin Kai, sun kai farmaki dajin Sambisa, inda suka ƙwato makamai da alburusai masu yawa.

Wata majiya ta bayyana cewa sojojin, sun kai samame yankin Ukuba tare da bataliya ta musamman ta 199 da kuma ‘yan sandan JTF domin bincike da ƙwato makaman da ‘yan ta’adda suka ɓoye.

Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Edo Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi

Da suka isa wajen da misalin ƙarfe 12:10 na rana a ranar 1 ga watan Maris, sun tarar da cewa ‘yan ta’addan sun tsere, inda suka bar makamai da kayan yaƙi da dama, ciki har da injina daban-daban, bindigogi, bututun RPG, da wasu kayayyakin fashewa.

Sojoji sun ce wannan farmakin yana daga cikin matakan da suke ɗauka domin fatattakar ragowar ‘yan ta’adda daga dajin Sambisa da kuma ƙwato makaman da suka ɓoye a yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan ta adda

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Nabamamu a Zamfara

Dakarun Sojin ‘Operation FANSAN YANMA’, sun kama Ƙasurgumin Shugaban ’Yan Bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu, wanda ya addabi al’ummar Mada, Tsafe, da wasu yankunan Jihar Zamfara.

Dakarun sun kai farmaki Hegin Mahe, Ruwan Bore, garin Mada, a Ƙaramar Hukumar Gusau a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Cibiyar bincike ta nemi a tabbatar da dokar kare haƙƙin mata a Arewa Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano

Bayan musayar wuta, sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga, yayin da Nabamamu ya tsere zuwa cikin wani gida, amma daga ƙarshe dakarun suka cafke shi.

Bayan kama shi, ɗaya daga cikin yaransa, Bakin Malam, ya jagoranci kai harin ramuwar gayya wasu ƙauyuka, wanda ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa.

Sai dai dakarun sun mayar da martani, inda suka fatattaki ’yan bindigar, tare da ƙara jibge sojoji don tabbatar da tsaro a yankin.

Nabamamu, ya kasance almajiri ne, daga baya ya zama hatsabibin ɗan bindiga wanda ya yi sanadin ajalin mutane masu yawan gaske.

Ya jagoranci sama da mayaƙa 100, inda yake karɓar haraji daga hannun mazauna wasu ƙauyuka, kuma yana da alaƙa da masu yi wa wasu mahara safarar makamai a yankin.

Kama shi na iya rage ƙarfin ’yan bindiga a Zamfara, yayin da sojoji ke ƙara ƙaimi domin kawar da barazanar tsaro da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasancewar Zaman Lafiya Na Dogon Lokaci Tsakanin Sin Da Amurka Abu Ne Da Ya Zama Wajibi
  • Mahara sun yi basaja da kayan EFCC wajen sace mutum 10 a otal
  • Nijar: An Kashe Sojoji 11 A Wani Hari Na Kungiyar al-Ka’ida
  • Yan Ta’adda Sun kashe Sojojin Sa Kai Na Basij Biyu A Yankin Kudu Maso Gabacin Kasar Iran
  • Kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombiya za su hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila
  • Yawan ’Yan Kasashen Waje Da Suka Shigo Kasar Sin Ba Tare Da Biza Ba A Bara Ya Ninku
  • Kasashen Afrika Ta Kudu, Malasiya Da Colombia Zasu Hana Jiragen Ruwa Dauke Da Makamai Tsayawa A Tashoshin Jiragen Ruwansu
  • Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Nabamamu a Zamfara
  • An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya