Hisba ta kama wasu matasa ba sa azumi a Kano
Published: 2nd, March 2025 GMT
Hukumar Hisba ta Jihar Kano, ta kama wasu matasa da ba su yi azumi a ranar farko ta watan Ramadan ba.
Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar, Dokta Mujahideen Abubakar ne, ya tabbatar da kama matasan.
Sojoji sun ƙwato makamai a dajin Sambisa Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a BauchiHakazalika, ya tabbatar da cewa jami’an Hisba sun cafke su yayin sintiri da suka yi a sassa daban-daban na Kano.
Har ila yau, hukumar ta kama wasu matasa ku san 60 bisa laifin askin banza, wanda ta ce ya saɓa wa dokokin addini da al’ada.
Bugu da ƙari, an kama wasu direbobin Adaidaita Sahu da ake zargi da cakuɗa maza da mata a cikin abin hawa, abin da hukumar ta ce ba za ta yarda da shi ba.
Hisba ta ce za ta ci gaba da sintiri domin tabbatar da an kiyaye dokokin Shari’a a lokacin watan Ramadan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɓarayin waya a Kano
Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago.
Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar SakkwatoSai dai kakakin ’yan sandan ya ce wani abokin ɓarawon da suka yi yunƙurin aika-aikar tare ya tsere da wayar da suka sata.
SP Kiyawa ya ce bayan binciken da aka gudanar ne ’yan sanda suka cafke wani mai suna Abduljabbar Musa Sheka kan zargin sayen wayoyin hannu da aka sata.
Ya ƙara da cewa za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar sun kammala bincike.
Rundunar ta gargaɗi ’yan kasuwa da su zama masu lura da abokan hulɗar da suke mu’amala da su, yana mai cewa akan samu miyagu da suke sojan gona a matsayin masu sayen kayayyaki a kasuwa.
Kazalika, rundunar ta yi kira ga duk wani ɗan kasuwa da irin haka ta faru da shi da ya gaggauta kai rahoto ofishin ’yan sanda mafi kusa.