HausaTv:
2025-03-03@09:31:46 GMT

Masar ta ki amincewa da duk wani yunkuri na kafa gwamnatin ‘yan adawa a Sudan

Published: 2nd, March 2025 GMT

Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar Larabawa ta Masar ta yi watsi da duk wani mataki da ke kawo barazana ga hadin kan Sudan, ciki har da yunkurin kafa gwamnatin ‘yan adawa, saboda hakan zai kara dagula al’amuran siyasa da kuma kawo cikas ga kokarin hada kan kasar.

Alkahira ta bukaci dukkan bangarorin da su yi aiki mai inganci tare da cikakken tsari na siyasa, da nufin cimma daidaito da kuma maido da tsaro a fadin kasar.

Ta kara da cewa, “Masar ta bukaci dukkan sojojin Sudan da su ba da fifiko ga cin moriyar kasa mafi girma da kuma taka rawar gani wajen bullo da wani cikakken tsari da zai kawo hadin da daidaito ba tare da nuna banbanci ko tsoma bakin kasashen waje ba.”

Ministan harkokin wajen Sudan Ali Youssef al-Sharif ya tabbatar a karshen watan da ya gabata cewa “babu wanda zai amince da abin da ake kira gwamnatin hadaka a Sudan, kuma babu wata kasa da za ta amince da ita.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas: Matakin Netanyahu na hana shigar kayan agaji a Gaza keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne

Hamas ta tabbatar cewa “Shawarar da Netanyahu ya yanke na dakatar da shigar da kayan agajin da jin kai na kasashen duniya zuwa zirin Gaza, hakan na a matsayin laifin yaki da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.”

Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila lamba da ta dakatar da matakin da ta dauka na yunkurin halaka mutane fiye da miliyan 2, inda ta kara da cewa, bayanin  Netanyahu dangane da tsawaita matakin farko wani yunkuri ne na kaucewa yarjejeniyar, da kuma kaucewa shiga tattaunawa a mataki na biyu.

Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, Isra’ila ta sanar da dakatar da duk wani taimakon jin kai ga Gaza da kuma rufe hanyoyin shiga yankin, tana mai jaddada cewa “Isra’ila ba za ta amince da tsagaita wuta ba, ba tare da sakin dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su ba, kuma idan Hamas ta ci gaba da kin amincewa da hakan, to za a samu wani sakamako.

Hamas ta jaddada muhimmancin kashi na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta; duk da haka, “Isra’ila” ta sanar da cewa ta amince da shawarar Amurka na tsawaita wa’adin tsagaita bude wuta a halin yanzu har zuwa tsakiyar watan Afrilu, yayin da tattaunawar da aka yi a mataki na biyu ta kasa samar da sakamakon da ake bukata.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masar Za Ta Bayyana Shirin Sake Gina Gaza A Yayin Taron Larabawa
  • Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha
  • Hamas: Matakin Netanyahu na hana shigar kayan agaji a Gaza keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne
  • Nijar: An Kashe Sojoji 11 A Wani Hari Na Kungiyar al-Ka’ida
  • Kasar Masar Ta Tabbatrawa Falasdinawa, Tana Bayansu Kafin Taron Kasashe Larabawa
  • Ma’aikatar Tsaron Jama’ar Sin Na Matukar Adawa Da Barazanar Da Amurka Ta Yi Na Karin Haraji
  • An Yi Musayar Yawu A Tsakanin Shugabannin Kasashen Amurka Da Ukiraniya A Fadar White House
  • An kori ma’aikatan Microsoft saboda adawa da yahudawan sahyoniya
  • Gwamnatin Kano Ta Shirya Taron Bita Don Jami’an Watsa Labarai