HausaTv:
2025-04-22@07:14:26 GMT

Babban Sakataren MDD Ya Taya Musulmi Murnar Shiga Watan Ramadan

Published: 2nd, March 2025 GMT

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan.

Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma.

Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba su samu damar sake ganin watan ba.

Ga duk wadanda suka samu ganin wannan lokaci mai tsarki cikin halin gudun hijira da tashin hankali, ina so in bayyana sakon tausayawa a gare su.

Ina goyon baya ga duk wadanda ke cikin halin tsanani da wahala, tun daga Gaza da sauran yankuna, zuwa Sudan, Sahel da sauran su. Kuma ina mai ba da hadin kai da masu gudanar da Azumin watan Ramadan da yin kira ga zaman lafiya da mutunta juna. A duk watan Ramadan, na kan kai ziyarar hadin kai tare da yin Azumi tare da al’ummar Musulmi a fadin duniya.

 Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci.

A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga kowa.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: watan Ramadan

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya : Mutum 56 suka mutu a harin Benue

Hukumomi a jihar Benue dake Najeriya sun ce adadin wadanda suka mutu  a harin da ‘yan bindiga suka kai a hukumomin Ukum da Kogo ya kai 56.

Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, a wata ziyara a yankin ya shaidawa manema labarai cewa  adadin wadanda suka mutu a harin ya kai 56.

”A yanzu, mutum 56 ne suka mutu wadanda ba su ji ba su gani ba, da suka hada da iyaye da maza da mata da kananan yara”, in ji shi.

Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakai domin kawo karshen hare-hare a jihar.

Gwamnan ya ce tuni gwamnatin jihar ta kara tura jami’an tsaro zuwa yankunan domin kwantar da hankula.

Harin na zuwa ne kimanin mako biyu bayan wasu yan bindiga sun kashe fiye da mutum 100 a wasu hare-hare a jihar Plateau mai makwabtaka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wang Yi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabon Ministan Harkokin Wajen Sudan Ta Kudu
  • Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Zababbun Shugabannin Gabon Da Ecuador
  • Fafaroma Francis ya Rasu
  • Fursunoni 9 Sun Tsere Daga Gidan Gyara Hali A Jihar Kwara, An Cafko Guda Daya
  • Najeriya : Mutum 56 suka mutu a harin Benue
  • Rugujewar Gini A Legas: Adadin wadanda Suka Mutu Ya Kai Biyar, An Ceto 20
  • Ma’aikatar Kasuwancin Sin: Dole Ne Amurka Ta Daina Dora Laifi Kan Sauran Kasashe
  • JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar bana
  • Yadda Za Ku Hada ‘Mimi Fankek’
  • An Fara Bikin Ranar Sojin A Iran 18 Ga Watan Afrilu Tare Da Gudanar da Fareti A Gaban Shugaban Kasar