Hukumar NOA Ta Bukaci Al’umma Su Kara Hakuri Da Kaunar Juna
Published: 2nd, March 2025 GMT
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na watan Ramadan wajen tunanin abubuwan da za su amfani kasa baki daya.
Kodinetan hukumar na jihar Jigawa Mallam Ahmed Tijjani Ibrahim
ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.
Malam Ahmed Tijjani ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi addu’ar zaman lafiya, da tsaro da ci gaban jihar da kasa baki daya.
Ya bayyana watan Ramadan a matsayin wata mai alfarma da ake son musulmi su kara kusanta ga Allah SWT, ta hanyar tsarkake zukatansu.
Don haka Tijjani ya umarce su da su zama ’yan uwan juna, su kasance masu hakuri da kamun kai, da tausaya wa marasa galihu a cikin al’umma.
Ya kara da cewa, NOA za ta bi sahun gwamnatin jihar domin sanya ido da kuma lura da al’amuran da ke gudana a watan Ramadan na wannan shekara domin tabbatar da ganin komi ya tafi yadda ake bukata.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
Hisba ta kama wasu matasa ba sa azumi a Kano
Hukumar Hisba ta Jihar Kano, ta kama wasu matasa da ba su yi azumi a ranar farko ta watan Ramadan ba.
Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar, Dokta Mujahideen Abubakar ne, ya tabbatar da kama matasan.
Sojoji sun ƙwato makamai a dajin Sambisa Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a BauchiHakazalika, ya tabbatar da cewa jami’an Hisba sun cafke su yayin sintiri da suka yi a sassa daban-daban na Kano.
Har ila yau, hukumar ta kama wasu matasa ku san 60 bisa laifin askin banza, wanda ta ce ya saɓa wa dokokin addini da al’ada.
Bugu da ƙari, an kama wasu direbobin Adaidaita Sahu da ake zargi da cakuɗa maza da mata a cikin abin hawa, abin da hukumar ta ce ba za ta yarda da shi ba.
Hisba ta ce za ta ci gaba da sintiri domin tabbatar da an kiyaye dokokin Shari’a a lokacin watan Ramadan.