An Wallafa Littafin “Zababbun Rubutu Game Da Tattalin Arziki Na Xi Jinping” Kashi Na 1
Published: 2nd, March 2025 GMT
Kwanan nan, aka wallafa littafin “Zababbun rubutu game da tattalin arziki na Xi Jinping” kashi na 1 a kasar Sin, wanda kwalejin nazarin tarihi da adabi na kwamitin kolin JKS ya tace.
Littafin “Zababbun rubutu game da tattalin arziki na Xi Jinping” kashi na 1, ya kunshi muhimman ayyuka kuma na asali na rubutun Xi Jinping kan raya tattalin arziki daga watan Nuwamban 2012 zuwa Disamban 2024.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An ga watan Ramadan a Najeriya — Sarkin Musulmi
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin ranar Juma’a, wanda hakan ke nufin ranar Asabar, 1 ga watan Maris, ita ce daya ga watan Ramadan 1446 Hijira a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Sarkin Musulmi, ya karanta a fadarsa, ya bayyana cewa an samu sahihan bayanai daga kwamitocin ganin wata da shugabannin addinin Musulunci a sassa daban-daban na kasar nan.
An ga watan Ramadan a Najeriya —Sarkin Musulmi Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfaraa dalilin haka, ya ayyana fara azumin watan Ramadan daga safiyar Asabar.
Haka nan, hukumomin Saudiyya ma sun tabbatar da ganin watan, inda suka ayyana Asabar a matsayin daya ga watan Ramadan a kasar.
Kira Ga Musulmi
Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi riko da ibada, addu’a da taimakon marasa galihu a wannan wata mai alfarma.
“Yana da matukar muhimmanci a cikin wannan wata mu kasance masu sadaukarwa, taimakon mabukata da kuma yawaita addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaban kasa,” in ji shi.
Ya kuma bukaci masu hali da su tallafa wa talakawa da gajiyayyu, musamman da abinci da sauran kayayyakin bukatu domin saukaka musu azumi.