Kasancewar Zaman Lafiya Na Dogon Lokaci Tsakanin Sin Da Amurka Abu Ne Da Ya Zama Wajibi
Published: 2nd, March 2025 GMT
Jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya bayyana a cikin wani jawabi ta bidiyo da ya gabatar ga taron kolin jagorancin Sin na Duke-UNC a ranar 28 ga watan Fabrairu cewa, kasancewar zaman lafiya mai dorewa tsakanin Sin da Amurka a duniya, abu ne da ya zama wajibi kuma nauyi ne dake kan wuyansu.
Xie Feng ya jaddada cewa, idan kasashen biyu suka dauki juna a matsayin abokan hamayya, kuma suka shiga mummunar gasa, kasashen za su yi rashin nasara, kuma duniya za ta sha wahala.
Ya ce babban abin sawa a gaba shi ne, Amurka ta mutunta ka’idar Sin daya tak, da daidaita batun yankin Taiwan yadda ya kamata, bisa kudurorin dake kunshe cikin takardu uku da Sin da Amurka suka amincewa, da adawa da “‘yancin kan Taiwan”, da daina kyautata alaka tsakanin Amurka da yankin Taiwan, da daina taimakawa yankin Taiwan fadada tasirinsa a wajen kasashen duniya, yin amfani da Taiwan don yaki da Sin zai kawo cikas ga kansa.
Kungiyoyin dalibai na jami’ar Duke da jami’ar North Carolina a Chapel Hill ne suka gudanar da taron kolin jagorancin Sin na Duke-UNC tare.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Trump : “Mun yi ganawa mai kyau da Iran”
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana gamsuwarsa da yadda tattaunawa tsakanin kasarsa da Iran ke gudana, yana mai bayyana ta a matsayin mai matukar kyau.
Da yake magana da manema labarai a fadar White House jiya litinin, Trump ya ce tattaunawa da akayi da jami’an Iran sun yi matukar inganci.
A ranar 12 ga watan Afrilu ne aka gudanar da zagayen farko na tattaunawar wacce ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka a shiga tsakanin kasar Oman a birnin Muscat.
Haka zalika a ranar Asabar 19 ga watan Afrilu bangarorin sun yi wa ta biyu a birnin Rome na kasar Italiya, a shiga tsakanin kasar Oman.
kasashen biyu sun bayyana kwarin gwiwar cewa za a ci gaba da tattaunawa, inda za a sake gudanar da mataki na gaba a kasar Oman a ranar Asabar mai zuwa.
Kafin nan kwararu daga kasashen na Amurka da Iran zasu hadu a kasar Oman a gobe Laraba inda zasu tattauna game da shirin nukiliyar na Iran na zaman lafiya.