HausaTv:
2025-04-03@08:17:17 GMT

Jagora: Iran Tana Fuskantar  Makiya Na Waje Kafirar Da Munafikai

Published: 3rd, March 2025 GMT

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; al’ummar Iran tana fuskantar makiya kafirai da munafikai, amma kasar ba ta da matsala da sauran al’ummun duniya.

Har ila yau jagoran ya ce, alkur’ani mai girma yana kunshe da hanyoyin da ya kamata a yi mu’amala da dukkanin wadannan makiyan, da kuma lokacin da ya kamata a yi Magana da su, ko kuma lokacin da ya kamata a zare musu takobi.

” Dukkanin wadannan bayanan suna cikin al’kur’ani mai girma.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron karatun alkur’ani mai girma, a jiya Lahadi da dare, ya yi ishara da cutukan ruhi da su ka addabi bil’adama a wannan  zamanin da su ka hada hassada, rowa,mummunan zato, ganda da son kai, da kuma fifita manufa ta kashin kai akan ta al’umma, tare da bayyana cewa, a cikin alkur’ani mai girma da akwai magungunan dukkanin wadannan cutukan.

Jagoran juyin musuluncin ya kuma ce, a bisa mahanga ta musulunci abu na biyu mai muhimmanci bayan tauhidi da ilimi da kyautata alaka da Allah, shi ne shimfida adalci a cikin al’ummar musulmi.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran ta mayar wa Amurka martani kan barazanar kai mata hari

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari.

Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran.

Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa za su kai mata hari.

Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka

“Suna yi min barazana, kuma idan suka sake suka kawo min hari tabbas zan rama,” in ji shi.

Yayin wata tattaunawa a ranar Asabar ne Trump ya yi alƙawarin kai wa Iran ɗin hari matuƙar ba ta amince da yarjejeniyar makamin ƙare dangin ba.

“Idan ba su amince da sabuwar yarjejeniyar makaman ƙare dangin ba, za mu tada bama-bamai,” in ji Trump.

Sai dai bai bayyana ko Amurkan ce za ta kai harin ba ko kuma ƙawarta Isra’ila.

To sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, kakakin ma’aikatar wajen Iran Esmaeil Baqaei ya ce barazanar ta Trump a bainar duniya yana matsayin shugaban kasa abin mamaki ne, kuma babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron ƙasa da ƙasa.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matashi ya daɓa wa abokinsa wuƙa a kan budurwa
  • Tarayyar Afirka Tana Shiga Tsakanin Bangarorin Dake  Rikici  Da Juna A Kasar Sudan Ta Kudu
  •  Kasar Afirka Ta Kudu Tana Ci Gaba Da Bibiyar “Isra’ila” A Kotun Duniya Ta Manyan Laifuka
  • Babban daraktan hukumar IAEA, Rafael Grossi, zai ziyarci Iran cikin makwanni masu zuwa
  • Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF
  •  Larijani:  Dole Iran Ta Kera Makaman Nukiliya Idan Amurka Da Isra’ila Su Ka Kawo Ma Ta Hari
  • Arakci: Abokan Gaba Za Su Yi Nadamar Yi Wa Iran Barazana
  • Iran ta mayar wa Amurka martani kan barazanar kai mata hari
  • Jagora : A yau, duniyar musulmi tana bukatar hadin kai
  • Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi