An Yi Jana’izar Shugaban Kasar Namibia Da Ya Samo Mata ‘Yanci
Published: 3rd, March 2025 GMT
A ranar Asabar din da ta gabata ne dai aka yi jana’izar Sam Nujoma wanda shi ne ya samo wa kasar ‘yanci bayan tsawon shekaru na gwgawarmaya.
Mahalarta jana’izar ta Nujoma sun kunshi iyalansa, mata,’ya’yan da jikokin, sai shugabannin kasashen Afirka na da, da masu ci.
A yayin jana’izar an bayyana Nujoma a matsayin wani gwarzo na fada da mulkin mallaka da tsarin wariya da ya kare nahiyar ta Afirka.
Shugaban kasar Namibia mai ci a yanzu ya bayyana Nujoma da cewa; Gwarzo ne da za a rufe shi a cikin makabartar da gwarazan kasar suke kwance. Kuma shi na musamman ne daga cikin ‘ya’yan wannan kasa, sannan kuma dan juyin juya hali.
Mahalarta jana’izar dai sun fito ne daga kowace kusurwa ta kasar Namibia,inda su ka taru a makabartar da ake rufe gwarazan kasar a birnin Waindhoek, domin yin jinjina da ban girma na krshe ga tsohon shugaban kasar wanda ya rasu yana dan shekaru 95.
Nujoma ya yi shugabancin kasar a zango uku daga 1990 zuwa 2005, tare da shimfida zaman lafiya da tsaro a cikin kasar.
An dauki kwanaki 21 ana juyayin rasuwarsa a gwamnatance, tare da yin kasa-kasa da tutar kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dakarun IRGC Suna Cikin Shirin Ko Ta Kwana Don Kare JMI Daga Makiyanta
Brigadier General Ali Mohammad Naeini, kakakin dakarun dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar ya bayyana cewa dakarunsa a shirye suke fiye da ko wani lokaci wajen kara kan iyakokin JMI daga makami.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran Naeini yana fadar haka a yau Talata a wani taro da kafafen yada labarai a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa a dai-dai lokacinda kasar ta cika shekaru 46 na nasarar juyin juya halin musulunci a kasar dakarun na IRGC suna cikin shirin da basu taba irinsa ba don kare kan iyakokin JMI.
Kafin haka, a farkon wannan watan jami’an gwamnatin JMI sun bayyana cewa kasar tana cikin shiri mai kyau na kare kan iyakokin kasar mai tsarki, sannan daga karshe sun bayyana cewa tsaron kasar jan layi ne ga makiya, don haka makiya sun yi hattara, kuma babu tattaunawa kan sa.