HausaTv:
2025-03-03@16:57:58 GMT

Masar Za Ta Bayyana Shirin Sake Gina Gaza A Yayin Taron Larabawa

Published: 3rd, March 2025 GMT

Babban jami’in diplomasiyyar kasar Masar ya sanar da cewa; Shirin da kasarsa take da shi na sake gina Gaza, abu ne mai yiyuwa a aikace, kuma za a aiwatar da shi ba tare da an kori mutane su bar Gaza ba.

Badr Abdul’adhy,  ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da fira ministan gwmanatin kwarya-kwaryar Falasdinu gabanin yin taron kasashen larabawa a birnin alkahira.

Ministan harkokin wajen kasar ta Masar ya ce; “Hanya daya tilo ta kawo karshen yawan fadace-fadace, shi ne a  cusa wa Falasdinawa fatan jin cewa,abinda suke mafarki da shi mai yiyuwa ne a aikace,wanda shi ne kafa ‘yantacciyar kasarsu.”

Haka nan kuma ya ce; Shirin da Masar take da shi na sake gina Gaza, mai yiyuwa ne a aikace, kuma cikin wani matsakaicin zango na lokaci, bai kuma bukatar a ce sai mutane sun bar kasarsu.”

 Wannan shirin na Masar dai ya zo ne bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya  ce za a kori Falasdinawa su miliyan biyu daga Gaza saboda sake ginata da kuma yin wasu manyan gine-gine na kasuwanci.

Kalaman na shugaban kasar Amurka sun fuskanci mayar da martani mai tsanani daga Falasdinawa, kasashen Larabawa, da kuma  wasu kasashen turai.

A nashi gefen, Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ya bayyana fatansa na samun cikakken goyon bayan kasashen larabawa domin aiwatar da shirin na kasar Masar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Masar ta ki amincewa da duk wani yunkuri na kafa gwamnatin ‘yan adawa a Sudan

Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar Larabawa ta Masar ta yi watsi da duk wani mataki da ke kawo barazana ga hadin kan Sudan, ciki har da yunkurin kafa gwamnatin ‘yan adawa, saboda hakan zai kara dagula al’amuran siyasa da kuma kawo cikas ga kokarin hada kan kasar.

Alkahira ta bukaci dukkan bangarorin da su yi aiki mai inganci tare da cikakken tsari na siyasa, da nufin cimma daidaito da kuma maido da tsaro a fadin kasar.

Ta kara da cewa, “Masar ta bukaci dukkan sojojin Sudan da su ba da fifiko ga cin moriyar kasa mafi girma da kuma taka rawar gani wajen bullo da wani cikakken tsari da zai kawo hadin da daidaito ba tare da nuna banbanci ko tsoma bakin kasashen waje ba.”

Ministan harkokin wajen Sudan Ali Youssef al-Sharif ya tabbatar a karshen watan da ya gabata cewa “babu wanda zai amince da abin da ake kira gwamnatin hadaka a Sudan, kuma babu wata kasa da za ta amince da ita.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Yamen Ta Gargadi HKI Da Amurka Kan Cewa Tana Sa Ido A Kan Abinda Ke Faruwa Da Tsagaita Wuta A Gaza
  • Lavrov Ya Yi Watsi Da Batun Aike Wa Da Dakarun Zaman Lafiya A Kasar Ukiraniya
  • Za A Gudanar Da Taron Manema Labarai Na Taro Na Uku Na NPC Karo Na 14 A Ranar 4 Ga Maris
  • Masar ta ki amincewa da duk wani yunkuri na kafa gwamnatin ‘yan adawa a Sudan
  • Kasar Masar Ta Tabbatrawa Falasdinawa, Tana Bayansu Kafin Taron Kasashe Larabawa
  • Iran Da Haddiyar Daular Larabawa Sun Gudanar Da Taron Kwamitin Siyasa Da Al-adu Na Kasashen Biyu
  • Yemen Ta Ce A Shirye Take Ta Koma Yaki Idan Yaki Ya Sake Barkewa A Gaza
  • Habasha Da Somaliya Sun Tattaunawa Hanyoyin Sake Mayar Da Alaka
  • Kasashen Afrika Ta Kudu, Malasiya Da Colombia Zasu Hana Jiragen Ruwa Dauke Da Makamai Tsayawa A Tashoshin Jiragen Ruwansu