Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda
Published: 3rd, March 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ɗora laifin ɓacewar bindigo 3,907 a hannun jami’anta a kan sakaci da kuma ƙarancin iliminsu game da kula da makamai.
Da take ƙarin bayani kan yawaitar ɓacewar bindigon, rundunar ta ɗora laifin ci gaban matsalar a kan abin da ta kira “sakacin” manyan jami’ai wajen tura ’yan sandan da ba su san ciwon kansu ba wajen aiki.
Rundunar ta bayyana takaicinta ne a wata takardar cikin gida daga “TERROFOR ABUJA” wanda wakilinmu ya yi katarin samu a ranar Lahadi.
Takardar ta fito a yayin da Majalisar Dattawa take gudanar da bincike kan rahoton Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya da ya nuna manyan bindigon ’yan sanda 3,907 sun ɓace.
A kan haka ne Kwamitin Majalisar mai kula da Kayan Gwamnati ya yi wa Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetekun da Mataimakin Sufeto-Janar mai Kula da Kuɗaɗe, Kasafi da Kayan Gwmanati, Suleiman Abdul, tambayoyin titsiye a kan ɓacewar bindigon.
Daga bisani kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fito ya bayyana cewa ɓata-gari ne suka yi awon gaba da bindigogin da ake magana a kai.
Ya kuma yi zargin cewa akwai aringizo a adadin da rahoton Babban Mai Binciken Kuɗin ya bayar na bindigogin da suka ɓace.
Sai dai kuma a wani saƙon cikin gida da Rundunar ta aika mai lamba CQ: 2400/DOPS/ CTU/FHQ/ABJ/VOL. 10/90, zuwa wa rassanta, ta gargaɗi manyan jami’anta cewa za su yaba wa aya zaƙi idan suka sake irin haka ta ƙara faruwa a ƙarƙashin jagorancinsu.
Saƙon ya kuma umarci manyan jami’an rundunar da su riƙa bayar da rahoton duk makaman da ke ƙarƙashin kulawarsu kafin ko a ranar 23 na kowane wata.
Rundunar ta aike saƙon ne ga sassauta da ke Kano da Maiduguri da Legas da Fatakwal da Abuja da Aba da Warri da Damaturu, ta gargaɗi manyan jami’anta cewa za su yaba wa aya zaƙi idan suka sake irin haka ta ƙara faruwa a ƙarƙashin jagorancinsu.
Sauran su e: Bauchi, Enugu, Jos, Minna, Kano, Yola, Ibadan, Owerii Makurdi, Lokoja, Gusau, Gombe, Lafia, Ilorin, Yenagoa, Uyo, Okija, Kaduna da Uburu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda manyan jami Rundunar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sanda
Rundunar ’yan sanda ta nemi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a Jihar Kogi.
Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar da gangamin siyasa da gwamnatin jihar ta yi ranar Litinin.
HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi“A sakamakon rahoton sirri kan barazanar tsaro a jihar Kogi da ya sanya hana duk wani gangami da jerin gwano da gwamnatin jihar Kogi ta yi, rundunar ‘yan sandan na kira ga wadanda suka shirya gangamin a Okene da su jingine irin wannan taron domin samar da zaman lafiya a Jihar Kogi.
Sanarwar ta ce, “kiran a jingine gangamin ya zama dole ne bisa rahotannin sirri da muka samu dangane da ƙoƙarin wasu ɓata gari na karkatar da gangamin zuwa wani abu daban da ka iya jefa jihar cikin tashin hankali.
“Saboda haka rundunar ’yan sandan ba za ta zura ido ta bar duk wani abun da zai jefa jihar mai zaman lafiya zuwa tashin hankali ba,” in ji sanarwar.
A watan da ya gabata ne dai zauren Majalisar Dattawan Nijeriya ya dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bisa zargin rashin da’a, kan sauya mata matsugunni da ta ce an yi ne ba bisa ka’ida ba kuma tta alakanta shi da zargin da take yi wa shugaban majalisar, Godswill Akpabio da cin zarafi da neman ta da lalata.