Saudiyya ta buɗe shafin rajistar masu Itikafi
Published: 3rd, March 2025 GMT
Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar.
A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi.
Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar za su cika domin samun gudanar da ibadar a kwanaki 10 ma ƙarshen watan Ramadan a masallatan Haramin Makkah da Madina da sauransu masallatan ƙasar.
Bayanan da ake buƙata sun hada da:
Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan MDD ta taya Musulmi murnar zuwan watan Ramadan1- Ƙasar mutum: Ta asali ko inda yake zama. Sanarwar ta bayyana cewa wajibi ne mai yin rajistar ya kasance ɗan ƙasar Saudiyya ko ya mallaki takardar iznin zama a can.
2- Wurin yin rajista: Wajibi ne mutum ya kasance a Saudiyya a lokacin da zai yi rajista, domin wanda ke wajen ƙasar ba zai iya shiga shafin ba.
3- Shekaru: Wajibi ne mai yin Itikafi ya shekarunsa su kai aƙalla 18.
4- Yanayin lafiya: An buƙatar ya kasance cikin ƙoshin lafiya ta yadda zai iya gudanar da ibada ba tare da wahala ba. Za a yi wa mutum gwajin duk wasu cututtuka masu tsanani. Idan mutum na buƙatar kulawa ta musamman, wajibi ne ya bayyana a yayin yin rajista.
5- Wa’adin Itikafi: Dole ne mutum ya bai ka’idar kwanakin da ya ɗiba na Itikafi. Lokacin ya fara ne daga ranar 20 ga watan Ramadana zuwa bayan Sallar Isha’ ta ranar jajibirin Ƙaramar Sallah.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ramadana Saudiyya yin rajista
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗi na N54.99trn
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da ya kai Naira tiriliyan 54.99.
A ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025, Majalisar Dokoki ta amince da kasafin bayan tattaunawa da nazari a kansa.
Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano Gwamnatin Sakkwato ta nemi malaman Jami’a su janye yajin aikiA baya dai, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin da ya kai Naira tiriliyan 49.7, amma daga bisani aka ƙara adadin kuɗin.
Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin a ranar Juma’a, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Kasafin kuɗin na 2025 ya ninka wanda aka yi a bara, wanda ya tsaya a Naira tiriliyan 27.5, da ƙarin kashi 99.96 cikin 100.