Gwamnatin Yamen Ta Gargadi HKI Da Amurka Kan Cewa Tana Sa Ido A Kan Abinda Ke Faruwa Da Tsagaita Wuta A Gaza
Published: 3rd, March 2025 GMT
Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta gargadi HKI da kuma Amurka kan cewa, tana sanya ido a kan yadda suke sabawa yarjeniyar budewa juna wuta da suka cimma da su. Musamman yadda HKI ta sabawa yarjeniyar a mashigar Rafah na barin abinci ya shiga Gaza, da kuma bukatar sake tattauna wasu al-amura a yarjeniyar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran nakalto Hazem Al-asad mamba a majalisar siyasa ta kasar Yemen, yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, kungiyar a shirye take ta sake shiga yaki da Amurka, a duk lokacinda suka yi kokarin cutar da mutanen Gaza.
Al-Asad ya gargadi gwamnatin Amurka da masu goyon bayan HKI a duk wata cutarwa da zata yiwa mutanen Gaza.
Har’ila yau, wani mamba a majalisar, Nasir-Addeen Amir ya bayyana cewa idanummu na kan abubuwan da suke faruwa a Gaza, sannan hannayenmu suna kan na’urorin bude wuta a kan dukkan abubuwan da suka shafi HKI da Amurka, don kare mutanen Gaza.
Amir ya kara da cewa dukkan makamai masu linzami na kasar Yemen su na cikin shirin komawa yaki idan HKI ko kawayenta suka sake farwa mutanen gaza.
Ya kuma kammala da cewa mayakan ansarullah za su sake budewa jiragen ruwa masu zuwa HKI wuta a tekun maliya da sauran wuraren da ta kaiwa hare-hare a baya bayan an fara yakin Octoban shekara ta 2023.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kwararrun Masana Sun Gargadi Kan Karkatar da Kudaden Fansho Na Biliyan ₦ 758
An shawarci gwamnatin tarayya da ta sanya ido sosai kan yadda za a biya ariyas na kudaden fansho da suka kai biliyan ₦758.
Wani masani kan harkokin kudi, Farfesa Yushau Ibrahim Ango ne ya bayar da wannan shawarar a Kaduna yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa PENCOM ta yi alkawarin kammala biyan kudin cikin watanni uku.
Farfesa Yushau Ango ya bayyana cewa, takardun lamuni yawanci kayan aikin kudi ne na dogon lokaci da ake samu daga masu saka hannun jari don warware basussukan da ake bin gwamnati, wanda yakan dauki lokacin da aka kayyade.
Ya nuna damuwarsa kan cewa bai kamata a rika rike irin wadannan kudade a bankunan kasuwanci da masu kula da fansho suka yi ba saboda wata manufa ta daban, yana mai jaddada cewa ba za a amince da duk wani mataki da aka dauka ba.
Masanin harkokin kudi ya kuma jaddada bukatar hukumomin da abin ya shafa su bi umarnin shugaban kasa tare da tabbatar da biyan basussukan fansho ba tare da bata lokaci ba.
SULEIMAN KAURA