Masu fasahar gina jiragen sama a kasar Iran sun samar da wani sinadari wanda ake kira ‘Smart Magnesium’ wanda ake iya rage nauyin jiragin sama da shi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu binciken na cewa sun samar da wani sinadari wanda baya sanya ‘magnesium Alloy’ a jikin jiragen sama tsatsa, kuma idan an rufe jikin jirgi da shi zai rage nauyinsa.

Banda haka zai kyautata yanda jirage zasu sarrafa makamashin jirgin.

Rahoton ya kara da cewa wannan kirkirar ya na da muhimmanci a kamfanonin kera jiragen sama, da kuma samar da  injuna, saboda zai kara dadewar jikin jiragen sama, kafin yayi tsatsa. Har’ila yau ya kuma taimaka wajen rage nauyin jikin jirgin.

Banda haka sabon fasahar da aka gano dai, zata tsawon lokacin amfani da jikin  fiye da yadda yake a yanzun. Labarin ya kammala da cewa Wannan fasahar zai taimakawa jiragen sama da kuma kumbo masu zuwa sararin samaniya.

Roqaieh Samadian-Fard, kwararre a wannan fannin ya bayyana cewa kafin haka ana samun matsalar tsatsar jikin jiragen sama da sauri, idan an kwatanda da wannan sabon sinadarin.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: jiragen sama

এছাড়াও পড়ুন:

An Fara Amfani Da Dandalin Samar Da Bayanai Na Kasar Sin

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ramadan: Hon Jaji Ya Ƙaddamar Da Tallafin Abinci Ga Mutane Sama Da 500,000 A Zamfara
  • An Fara Amfani Da Dandalin Samar Da Bayanai Na Kasar Sin
  • Kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombiya za su hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila
  • Masana’antar Kannywood: Da Tsohuwar Zuma… -Fassarar Farfesa Uba Adamu
  • An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe
  • Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata A Sani A Kan Kiwon Kifi
  • Japan Ta Kirkiro Da Sabuwar Kimiyyar Samar Da Ingantacciyar Madarar Shanu
  • Kasashen Afrika Ta Kudu, Malasiya Da Colombia Zasu Hana Jiragen Ruwa Dauke Da Makamai Tsayawa A Tashoshin Jiragen Ruwansu
  • Kwastam Da Hukumar NPA Sun Kulla Hadakar Bunkasa Ingancin Aiki A Tashoshin Jiragen Ruwa