Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wa ta sabon tattaunawa da kuma sauya yarjeniyar tsagaita wuta da aka cimma da HKI dangane da yaki a Gaza ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmoud al-Mardawi wani babban jami’in kungiyar yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘ba zamu tsawaita kashi na farko na yarjeniyar ba, haka ma ba za mu amince da gabatar da sauye –sauye a cikin yarjeniyar ba.

Mardawi yace HKI za ta karbi fursinonin da suka rage a hannun Hamas kadai ne, ta hanyar ko tsarin da yarjeniyar ta amince da shi. Ya ce: Benyamin Natanyahu yana, cikin dimwa idan ya na son amfani da yunwa a matsayin makami don samun abinda ya kasa samu da makamai ba. HKI ta bada sanarwan cewa za ta dakatar da dabbaka yarjeniyar sulhu da Hamas bayan an kammala kashi na farko na Yarjeniyar, kuma zai dakatar da shigar abinci yankin Gaza idan an kammala kashi na farko na yarjeniya.

Kafin haka Netanyahu ya ce ya amince da shawarar da jakadan shugaban kasar Amurka Donal Trump, Steve Witkoff ya gabatar na tsawaita bangare na farko a yarjeniyar saboda watan Ramadan.

Kakakin kungiyar Hamas Hazem Wassem ya ce: kungiyar tana tuntubar masu shiga tsakani a aiwatar da yarjeniyar , a kai a kai, don ganin al-amura sun koma kamar yadda yakamata.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a yarjeniyar

এছাড়াও পড়ুন:

Isra’ila na karbe yankuna a zirin Gaza

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sojojin kasar na karbe iko da wasu yankunan zirin Gaza, a wani mataki na kara matsin lamba kan kungiyar Hamas domin tilasta ta sakin mutanen da ta ke garkuwa da su.

“Muna karbe zirin Gaza tare da kara matsin lamba mataki-mataki domin tilasta su mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su,”inji  Netanyahu a wani faifan bidiyo da ofishinsa ya fitar.

Ya kara da cewa, Sojoji na karbe yankuna, suna kai farmaki kan ‘yan wadanda ya danganta da ‘yan ta’adda in ji shi, yana mai sanar da samar da wata sabuwar hanya karkashin ikon Isra’ila don raba garuruwan Khan Younis da Rafah (kudu).

Tunda farko dama ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya sanar a Larabar nan cewa, kasarsa ta fadada kaddamar da hare-haren soji a sassan zirin Gaza, yana mai barazanar dakarun Isra’ila za su kwace karin yankuna a zirin da nufin samar da yankuna masu tsaro da za su raba Isra’ila da wurare masu fama da tashin hankali.

Cikin wata sanarwa, mista Katz ya ce matakin fadada ayyukan sojin zai kunshi fadada kwashe mutane daga yankunan da ake dauki ba dadi a Gaza.

Isra’ila dai ta kawo karshen wa’adin tsagaita wuta na watanni 2 tun a ranar 18 ga watan Maris da ya shude, inda ta koma kaddamar da munanan hare-hare ta sama da kasa kan wuraren da Falasdinawa ke fakewa.

A jiya Talata, hukumomin lafiya a Gaza sun ce kawo yanzu sabbin hare-haren sun sabbaba rasuwar Falasdinawa 1,042 tare da jikkata wasu 2,542, yayin da rikicin da ya barke tun daga watan Oktoban shekarar 2023 zuwa yanzu, ya haddasa jimillar asarar rayukan Falasdinawa 50,399, tare da jikkata wasu 114,583.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka Ta Daba Wa Kanta Wuka Bisa Karin Harajin Da Ta Yi 
  • Isra’ila na karbe yankuna a zirin Gaza
  • Araghchi : Iran a shirye take don tattaunawa amma barazanar soji daga Amurka na dagula yanayin’
  • Kisan Mafarauta: Babu wanda aka kai wa harin ramuwar gayya a Kano — Ƙungiyoyin Matasa
  • Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha
  • Babu dokar da na karya saboda yin taron a mazaɓata — Natasha
  • Gangamin da zan yi a mazaɓata babu fashi — Natasha
  • Kungiyar “Amnesty” Na Zargi Netanyahu Da Aikata Laifukan Yaki
  • Kungiyar RED CROSS Ta Duniya Ta Yi Allawadai Da HKI Saboda Kissan Likitoci 8 A Asbitin Rafah
  • Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran