HausaTv:
2025-03-03@17:59:11 GMT

Kissoshin Rayuwa Sirar Imam Alhassan(99)

Published: 3rd, March 2025 GMT

99-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani  mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Mutahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu.  …Music—–music……music…

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).

Mun kawo maku yanda aka fidda Imam Ali (a) da karfi daga gidansa don ya yi bai’a ga Khalifa na farko amma yaki amincewa da hakan, sai Khalifa na farko, don tsoron fitina sai ya barshi ya tafi, Amma kuma bayan haka sai ya kwace gonar Fadak ta Zahra (a). Sannan a lokacinda ta nemi a dawo mata da ita, sai ya nemi ta kawo shaidu kan cewa manzon All..(s) ya bata gonar kyauta.

Mun kuma bayyana cewa: A addinin musulunci, ba’a tambayar wanda abu ya ke hannunsa shaida, wanda yake neman ya fidda shi daga hannun wanda yake rike da shi ne zai kawo shaidu.

Gonar Fadak tana hannun Zahra (s) tun shekara ta 7 bayan hijira, a wani addini ne za’a nemi ta kawo shaida?

Amma tunda suna jin tsaron kada Aliyu (a) ya yi amfani da kudaden gonar don neman hakkinsa, sai suka kwaceta ba tare da wata hujja ta shari’a ba.

Mun kuma bayyana yadda gonar ta shiga hannun ta (s). Ayar alkur’ani ce ta sauka ta mallakarwa manzon All..(s) gonar da farko, Sannan wata ayar din ta sauka ta mallakarwa Zahra (s). Ana karanta wadannan ayoyi a cikin Alkur’ani mai girma da kuma dalilan saukarsu a cikin tafsirin wadannan ayoyi. Wadanda suke tabbatar da cewa gonar Fadak, gona ce ta yahudawan Fadak suka sulhunta da manzon All..(s) don haka ta zama tashi, sannan shi kuma tare da saukar wata ayar ya bada ita ga Zahrah (s).

Wasu malaman da dama sun tabbatar da cewa Abubakar bai kwace, gonar fadar daga hannun Zahra(s) ba, sai don ya karya Aliyu(a) ta bangaren tattalin arziki.

Ance ana girmama mutum ta yayansa da danginsa a bayansa, yaya idan mutumin manzon All…(s). mafificin halittun All..T, ba sai mun kawo ayoyin alkur’ani da suka tabbatar da tsarkin diyarsa Fatimah (s) ba, ba sai mun kawo hadisan manzon All…(s) wadanda suka bayyana matsayinta a wajen All…T ba. Idan muka ce wannan diyar wannan mutum sharifi ne, jikan manzon All..(s) ta diyarsa Fatima (s) ya isa a girmama shi, ko da mai yin kuskure ne kuwa, tunda ba dukkan sharifai ne ma’asumai ba.

Muna girmama jikokin Fatimah (s) a cikin al-ummar musulmi, ta yaya, ba zamu girmama kakarsu Fatimah (s) ba?.

Amma duk da haka, Fatiman (s) ta kawo mijinta Aliyu dan Abitalib (s), wanda manzon All..(s) yake fada dangane da shi “Aliyu yana tare da Al-kur’ani, Alkur’ani na tare da Aliy (a). Ya zo ya shaida mata kan cewa manzon All..(s) ya ba ta gonar Fadak kyauta bayan yakin Khaibara a shekara ta 7 bayan hijira, banda haka ta kawo Ummu Aimanu, diyar gidan manzanci, wacce da dama sun san cewa ya yi mata bushara da aljanna, ta zo ta shaida mata kan cewa manzon All..(s) ya bata gonar Fadak kyauta, amma sai Khalifa na farko bai amince da shaidunta ba. Ya yi watsi da shaidun nata (s).

Wannan ma, ya sabawa shari’a saboda idan ana shari’a kan dukiya ne, ko dangane da abinda ya shafi duniya, to ana tabbatar da shi da shaida guda da kuma rantsuwa. Idan mai da’awa ya kawo shaida guda, alkali yana iya karban rantsuwa ya mallakar masa dukiyan da yake nema ko ya ce nashi ne. Idan yayi rantsuwa ya wadar masa daga shaidu biyu.

Don haka Khalifa na farko ya sanya iyalan gidan manzon All..(s) cikin matsaloli, da bakin ciki, tun idanunsu basu bushe daga hawayen wafatin mahaifinta ko kakansu manzon All..(s) ba. Lalle wannan ba sakawa manzon All..(s) da Alkhairi ba. Ina ma da a ce, ya yi duk yadda zai yi ya kaucewa fushinta (s), ta yaya zai toshe mata dukkan kofofin na maida hakkinta?.

Amma al-amarin kamar yadda wani babban malami kuma malami a makarantar Baghadaza ta (gharbiyya) ya ke fadawa dalibinsa Ibn Abil Hadid (mai sharhin Littafin Nahjul Balagha), a lokacinda ya tambaye shi. Shin Fatimah(s) ba ta da gaskiya ne? a cikin al-amarin gonar Fadak?

Sai  ya ce: Tana da gaskiya? Sai ya ce: To me yasa bai bata gonar Fadak ba?, al-hali ta na da gaskiya?

Sai Malamin ya yi murmushi, (duk da cewa mutum ne wanda bai cika murmuce ko wargi da wasa ba.  Sai ya ce: Da ya bata gonar Fadak, don ya san tana da gaskiya, da kuwa, gobe za ta zo, ta ce Khalifanci na mijinta ne. Don haka sai ta kauda shi daga kujerar khalifanci, sannan a lokacin da ta yi hakan, bai isa kuma ya ce ko me ba don ya rika ya gasgatata.

Amma wannan al-amarin ya sa Khalifa na farko ya yi nadama a cikin sauran rayuwarsa, sannan a karshen yaruwarsa ya ambaci hakan. Inda aka ruwaito shi ya na cewa:….ina ma da bai aika a je a farwa gidan Aliyu da Fatimah (s) ba!, ko da kuwa sun rufe gidan don su yake ni ne!.

…………………Music…………………..Music………………

Hakika,a lokacin ya wulakanta diyar manzon All..(s) ya kuma kwace hakkinta, ya ki sauraron hujjojinta da shaidunta, tun lokacin abin ya na damunsa a cikin zuciyarsa har zuwa lokacin wafatinsa ya na nadamar hakan.

Shi ya sa a lokacin da shi da abokinsa suka ji labarin cewa ba ta da lafiya, sai suka je gidanta, suka nemi izinin shiga wajenta har sau biyu ta ki amincewa. Daga karshe suka yi tawassuli da Imam Ali (a) ya shigo da su wajenta(s).

A nan ne sai Imam Ali (a) ya shiga wajen ta (s) ya nemam masu izinin shiga wajenta, ta ki amincewa, sai da ya matsa, sai ta amince don alkawalin da yayi masu zai shigo da su wajenta.

Sannan a lokacinda suka shiga wajenta ta ki ta amsa sallamarsu, taki ta yi ma su magana,    sai suka matsa, sai ta ce su fadi abinda za su fada sai Khalifa na farko ya ce: Ya ke masoyiyar manzon All…(s), Wallahi Lalle dangin manzon All..(s) sun fi soyuwa a gareni kan dangi na, wallahi kinfi soyuwa a gareni kan diyata A’isha, wallahi na so ace ranar da babanki ya rasu, ni ma na rasu a rannan, kada in wanzu bayansa.. … har zuwa inda yake cewa… shin ki na ganin, da irin sanin da yi maki, da matsayinki, da daukakarki, sannan in hanaki hakkinki,? in hanaki gadonki, ?  Sai dai na ji manzon All..(s) ya na cewa:

{….mu bama gadarwa, duk abinda muka bari sadaka ne…}

Amma Zahra (s) ta karyata wannan hadisin a khudubarta da ta yi a gaban mutane a masallacin babanta (s). ta kawo hujjoji daga Alkur’ani mai girma kan cewa gadon annabawa dai dai yake da gadon sauran musulmi.  

Da ya kammala maganarsa sai ta juya ta na masu Magana tana cewa {Na hadaku da All..baku taba jin manzon All..(s) yana cewa: Yardar Fatima ya na daga cikin yardata ba ? kuma fushinta daga fushi na ba?, wanda ya so diyata Fatimah hakika ya so ni, wanda ya sami yardar Fatimah ya sami yardata, wanda ya fusata Fatimah ya fusatani?.

Sai suka amsa da cewa : Eee mun ji shi,}. Sai ta daga hannayenta sama tana cewa: Ina shaidawa All..da mala’ikunsa, kun fusatani, baku nemi yarda ta ba, ….har zuwa inda take cewa…Sannan lalle idan na hadu da manzon All…zan kai kararku a gabansa.

Sai Khalifa na farko ya tashi yana kuka, sai ta ce masa, {Na rantse da All..zan yi addu’a a kanka bayan sallolina..}

Wadan nan kalmominta (s), zafinsu, ya fi zafin duka da takobi, Khalifa na farko ya fita gidan yana kuka da hawayensa, kuma sun kasa samun yardarta (s) wanda yana daga cikin yardar All..T.

A hadisi, manzon All..(s) yana fadawa fatimah(s): Lalle All..yana fushi da fushinki, yana yarda da yardarki.

Don haka duniya ta kuntata ga Khalifa Abubakar, har sai da ya yi kuka don rage zafin bakincikin da ya same shi saboda fushinta(s), don ya kasa samun yardar tsoka daga tsokar jikin manzon All..(s). wanda kuma shi ne yardar All…T.

Wadan nan al-amura gaba daya sun faru a gaban Imam Hassan (s) tunda a cikin gidansu ya faru, kuma mahaifiyarsa ce diyar manzon All..(s) take fada masu hakan, a gabansa(s). Kuma sun bar tasiri a cikin zuciyarsa, har’ila yau  Imam Hassan (s) ya ga yadda mahaifiyarsa (s) ta yi bakinciki da wafatin mahaifinta manzon All..(s), kuma kakansa, (s), irin bakincin da ya kai ga, ana buga misali da ita, a bakin ciki a tsawon tarihin musulmi.    

Wata rana Anas Dan Malik ya shiga wajenta(s) bayan wafatin mahaifinta, sai ta kira shi, tace, Ya Anas, sai yace: Na’am ya diyar manzon All..(s): Sai ta ce masa: Ta yaya kuka zuba kasa a kan kabarin manzon All…(s), sai Anas ya fara kuka ya na zubar da hawaye don ta tunatar da shi wafatin manzon All..(s), don Anas ya na daga cikin wanda suka halarci jana’izar manzon All..(s).

Sannan a lokacinda wafatinta (s) ya zo, sai ta kira mijinta Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib(a) ta yi masa wasiyoyi da dama, daga ciki ta ce masa kada ya bar wanda baya sonta, ya kuma bayyana adawa gareta, yayi mata sallah. Don haka ne Amirulmuminina (a) ya yi mata wanka da Jana’iza a cikin dare, idanu sun yi barci, sai na yayanta(s), daga ciki har da Imam Hassan(a). Suna Kallon yadda mahaifinsu Amirul muminina (a) daga nesa ya na Sanya mata likkafaninta bayan yayi mata wanka,  bayan ya kammala sai ya kirasu su zo su yi bankwana da ita, sai suka zo, suna kuka suna sumbantar likkafaninta (s), kowa na kiran umma, umma. Umma…

A nan ne Imam Ali (a), bayan wadanda ya kira su, don yi mata salla suka is aba tare da hayaniya ba, sai ya tsaya bayan jana’izarta (s) sannan yayansa Imam Hassan da Alhussain (a) suka tsaya a bayansa sannan sauran masoya Iyalan gidan manzon All..(s) suka yi mata sallah, sannan suka sa ta a kabarinta a boye, don kada wani, daga cikin wadanda bata son su yi mata sallah su san inda kabarinta yake, su zo su tsaye a kan kabarin na ta(s).

Bayan da gari ya waye, mutane sun taru don yi mata sallah, sai suka sami labarin cewa ay an yi mata Jana’iza a cikin dare tare da wasiyyarta (s). Da dama sun yi bakinciki da rashin samun damar yi mata sallah. Imam Alhassan (s) ya na sane da dukkan wadan nan al-amura gaba daya.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata Fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Sai Khalifa na farko sai Khalifa na farko Khalifa na farko ya diyar manzon All ta gonar Fadak shiga wajenta masu sauraro tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Motocin Buldoza Suna Ta Rusa Gidajen Falasdinawa A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Kungiyar Hamas ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a yankin yamma da Kogin Jordan tana rusa gidajen Falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nur- Ashamsh, a ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Nihad Ashawish shugaban kwamitin mai kula da sansanin yan gudun hijirar yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa a jiya Asabar ce motocin Buldoza na HKI suka shiga unguwar Almanshiya suka rusa gidajen wasu Falasdinawa, sannan suka bata hanyoyi a unguwar.

Kamfanin dillancin labaran Abadulu na kasar Turkiya ya nakalti Ashawish yana cewa, sojojin HKI su kan tilastawa Falasdinawa fita daga gidajensu sannan su rusasu a gabansu. Tare da umurnin su fice daga yankin su je inda suka ga dama.

Hamas ta kammala da cewa da wannan aikin zamu fahinci cewa gwamnatin HKI tana son kara korar Falasdinawa daga kasarsu, musamman daga yankin yamma da kogin Jordan.

Kungiyar ta bukaci MDD ta dauki matakan da suka dace don hana yahudawan mamayar karin gidajen Falasdinawa a arewacin yankin yamma da Kogin Jordan.

A jiya Asabar kwanaki 21 cur Kenan gwamnatin HKI take rurrusa gidaje da lalata hanyoyi a garuwan Falasdinawa dake yankin yamma da kogin Jordan musamman garuruwan Tulkaram, da Jenin.

Majiyar asbitoci a yankin yamma da kogon Jordan sun bayyana cewa daga lokacin zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 64 sannan wasu dubbai an koresu daga gidajensu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yi Jana’izar Shugaban Kasar Namibia Da Ya Samo Mata ‘Yanci
  • Kasancewar Zaman Lafiya Na Dogon Lokaci Tsakanin Sin Da Amurka Abu Ne Da Ya Zama Wajibi
  • Motocin Buldoza Suna Ta Rusa Gidajen Falasdinawa A Yankin Yamma Da Kogin Jordan
  • Abubuwan Sha Domin Karin Ni’ima Ga Mata
  • Iran Da Haddiyar Daular Larabawa Sun Gudanar Da Taron Kwamitin Siyasa Da Al-adu Na Kasashen Biyu
  • ‘Yansanda Na Farautar Wadanda Suka Kashe Dalibi A Katsina
  • SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1
  • Yawan ’Yan Kasashen Waje Da Suka Shigo Kasar Sin Ba Tare Da Biza Ba A Bara Ya Ninku
  • MDD Ta Bayyana Cewa Yara Fiye Da 100,000 Ne Suka Ka Yi Rijistan Fara Karatu A Makarantun Gaza Na Sabuwar Shekarar Karatu