Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin noman rani ta hanyar amfani da rijiyoyin burtsatse a karamar hukumar Maigatari.

Hakan wani muhimmin mataki ne  na samar da abinci da zamanantar da noma a jihar Jigawa.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa gidan rediyon Najeriya ya ce, gwamnan ya bayyana cewa, aikin da ake amfani da shi ta hanyar amfani da hasken rana da kuma amfani da dabarun noman rani, yana yana taimakawa wajen yin noma a kowane lokaci na shekara tare da bunkasa tattalin arzikin manoma.

A cewarsa, shirin mai fadin hekta 10 wanda aka samar da rijiyoyin burtsatse na zamani guda hudu do  tallafa wa kananan manoma 80 kai tsaye, zai habbaka noman abinci tare da inganta rayuwar al’umma.

Gwamna Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatinsa na aiwatar da manufofinta guda 12, inda ya jaddada fadada ayyukan ban ruwa da suka hada da madatsun ruwa da rijiyoyin burtsatse.

Ya ce nan ba da jimawa ba za a kammala irin wadannan ayyuka a kananan hukumomin Birniwa da Kafin Hausa.

Namadi ya ce kasafin kudi na 2025 ya hada da kara ayyukan noman noman rani a Gumel, da Sule Tankarkar, da Gagarawa.

Ya kuma bayyana irin rawar da shirin ke takawa wajen rage dogaro da nomar damina kadai, tare da inganta ayyukan noma, da samar da karin kudaden shiga ga manoma.

 

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Noman Rani

এছাড়াও পড়ুন:

Saliyo Ta Kaddamar Da Cibiyar Likitancin Gargajiya Na Sin Ta Farko

An kaddamar da cibiyar likitancin gargajiya na Sin ta farko, ranar Juma’a a Freetown, babban birnin kasar Saliyo, wadda ta zama muhimmin mataki a yunkurin kasar na amfani da likitancin gargajiya na Sin domin amfanawa al’umma.

Kadammar da cibiyar ta biyo bayan kammala wani aikin binciken kiwon lafiyar al’umma a kasar wanda likitocin kasar Sin suka jagoranta, wanda ke da nufin tallafawa kasar inganta matakan kariya da maganin cututtuka gama gari kamar hawan jinni da ciwo mai tsanin.

Da yake gabatar da jawabi yayin bikin kaddamar da cibiyar, mataimakin ministan lafiya na kasar Saliyo Charles Senessie, ya yabawa dangantaka mai karfi dake tsakanin Sin da Saliyo a bangaren kiwon lafiya, musammam wajen amfani da likitancin gargajiya na Sin. Ya ce Saliyo ta samu nasarori wajen hada likitancin gargajiya na Sin da tsarin kiwon lafiya na kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masar : Za’a Gabatar Da Shirin Baiwa Falasdinawa Yancin Zama A Kasarsu
  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Gargadi Malaman Da Ba Sa Zuwa Aiki
  • Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Shirin Ciyarwar Na Watan Ramadan
  • Saliyo Ta Kaddamar Da Cibiyar Likitancin Gargajiya Na Sin Ta Farko
  • An Fara Amfani Da Dandalin Samar Da Bayanai Na Kasar Sin
  • An raba wa ma’aikatan gona babura 200 a Yobe
  • Noman Rani: Tinubu Ya Amince Da Fadada Madatsun Ruwa 12 A Nijeriya
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Masallacin Juma’a A Garin Samamiya Da Ke Birnin Kudu
  • Noman Dabino: Jigawa Ta Yi Hadaka Da Saudiyya