Wani mutum wanda aka bayyana a matsayin Abdulrashid Usman, ya yanke jiki ya mutu a yayin da yake buɗa-baki a yankin Babban Birnin Tarayya.
Wani shaida mai suna Suleiman Bala, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da aka ɗauki azumi, lokacin da mamacin da abokansa suke buɗe-baki a majalisarsu da ke yankin Kutunu a Ƙaramar Hukumar Gwagwalada.
Ya ce Usman da abokansa suna zaune a kan benci suna cin ’ya’yan itatuwa ne ya yanke jiki ya faɗi, rai ya yi halinsa.
Nan take abokan suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar cewa rai ya yi halinsa.
A cewarsa, marigayin, wanda yake cikin koshin lafiya, ya dawo daga Kaduna ganin buɗa-baki, daga nan ya je majalisarsu ya haɗu da abokansa, bayan an sha ruwa suna tsaka da buɗa-baki lamarin ya faru.
“Wani ɗan uwan marigayin ya ce mamacin ya dawo daga Kaduna kuma ya je shiga cikin abokansa inda suke annashuwa.
“Bayan kiran Sallah suna buɗa-baki lamarin ya faru,” in ji shaidar.
Ya ce an binne shi bisa tsarin addinin Musulunci.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Edo
Aƙalla fasinjoji 12 ne suka ƙone ƙurmus har lahira a wani mummunan hatsari da ya auku a kan titin Benin zuwa Auchi a Jihar Edo.
Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Edo, Cyril Mathew, ya tabbatar da aukuwar hatsarin.
Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi Abubuwan da ya kamata a sani game da azumin watan RamadanaYa ce wata mota ƙirar Toyota Hiace ce ta yi karo da babbar tifa.
A cewarsa, hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na asuba a ranar Asabar, a kusa da wani shingen sojoji da ke yankin Igueoviobo.
“Motar ta taso ne daga Zuba a Babban Birnin Tarayya tana kan hanyarta n zuwa Benin, amma ta yi karo da wata babbar tifa da ke kan hanyar zuwa Auchi.
“Duk fasinjojin da ke cikin motar sun rasa rayukansu,” in ji shi.
Mathew, ya ce ana zargin direban motar da gajiya yayin tuƙi, lamarin da ya sa ya fara barci a kan hanya, wanda hakan ya haddasa hatsarin.
Karon da motocin suka yi ya haddasa tashin wuta, lamarin da ya sanya fasinjojin zuka ƙone ƙurmus.
Sai dai direban babbar tifar da yaronsa sun tsira ba tare da sun ji rauni ba.
Kakakin ya shawarci direbobi da suke hutawa a duk lokacin da suka gaji domin gujewa aukuwar hatsari.