Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Shirin Ciyarwar Na Watan Ramadan
Published: 3rd, March 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyarwa a watan Ramadan na shekarar 2025 a hukumance, da nufin samar da abincin buda baki ga mabukata 91,000 a fadin jihar.
Shirin wanda zai dauki tsawon kwanaki 27 yana daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafawa dimbin al’ummarta a watan na Ramadan.
Mataimakin gwamnan jihar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo wanda kuma shi ne shugaban shirin, ya kaddamar da shirin a hukumance a cibiyar Dandali dake karamar hukumar Fagge.
Ya nuna jin dadinsa da yadda aka gudanar da shirin cikin kwanciyar hankali, tare da yin kira ga kamfanonin da abin ya shafa da su tabbatar da isar da abinci cikin lokaci da inganci a dukkanin cibiyoyin ciyar da abincin.
Za a aiwatar da shirin a cibiyoyin ciyar da abinci 91 da aka keɓe, inda aka tanadar da masu dafa abinci don ciyar da mutum 91,000 abinci a kowace rana.
Gwamnatin jihar Kano ta ware makudan kudade domin tabbatar da nasarar shirin, inda ta nuna aniyar ta na tallafawa marasa galihu a wannan wata na Ramadan.
Bikin kaddamar da shirin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da suka hada da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, da kwamishinan harkokin addini, Sheikh Tijjani Auwal.
Daga Khadija Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Sakataren MDD Ya Taya Musulmi Murnar Shiga Watan Ramadan
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan.
Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma.
Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba su samu damar sake ganin watan ba. Ga duk wadanda suka samu ganin wannan lokaci mai tsarki cikin halin gudun hijira da tashin hankali, ina so in bayyana sakon tausayawa a gare su.
Ina goyon baya ga duk wadanda ke cikin halin tsanani da wahala, tun daga Gaza da sauran yankuna, zuwa Sudan, Sahel da sauran su. Kuma ina mai ba da hadin kai da masu gudanar da Azumin watan Ramadan da yin kira ga zaman lafiya da mutunta juna. A duk watan Ramadan, na kan kai ziyarar hadin kai tare da yin Azumi tare da al’ummar Musulmi a fadin duniya.
Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci.
A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga kowa.