Aminiya:
2025-04-03@02:28:14 GMT

Hakar ma’adanai: ILO ta horas da masu ruwa da tsaki kan illar bautar da yara

Published: 3rd, March 2025 GMT

A wani yunkuri na kawo karshen bautar da kananan yara a Najeriya, Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO ) ta horas da masu ruwa da tsaki kan tsaron sana’o’i da kuma yakar bautar da yara a aikin hakar ma’adanai.

Kungiyar da ke kula da wurare hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ta shirya taron ne da nufin ķarfafa guiwar masu ruwa da tsaki domin kawo karshen bautar da yara a wuraren hakar ma’adinai a jihohin Neja da Osun.

Taron da ya gudanan daga ranar 18 zuwa 27 na watan Fabarirun 2025, wakilan gwamnati da kungiyoyin ma’aikata da shuwagabannin yankunan sun hallara, inda suka tattaun kan hanyoyin kawo karshen matsalar.

Kazalika an bai wa mambobin kwamitin sanya ido kan ayyukan bautar da yara na jihohin kayan aiki da za su taimaka musu wajen sanya ido kuma da kai rahoton game da bautar a kananan yara.

Miji ya amince saurayin matarsa ya tare a gidansu Ramadan: Coci ya ciyar da Musulmi 1,000 a Kaduna

A jawabinta, Daraktan kungiyar kwadago ta Najeriya, Dakta Vanessa Phala, wacce ta samu wakilcin mai kula da ayyuka na kungiyar ACCEL Africa, Misis Celine Oni, ta jaddada cewa za a aiwatar da dokoki da tsare-tsare da za su taimaka wajen kawo karshen wannan matsala.

Kudurin karfo na shirin ACCEL Africa shi ne, aiki tare da ma’aikatun kwadago da na bunkasa ayyuka da na noma, da na ma’adanai da dai sauransu.

Na biyu shi ne, daukar mataki kan sabubban bautar da yara a wuraren haķar ma’adanai, da kuma mai da hankali kan samar da kariya da kudade da kiwon lafiya da kuma aikin yi ga matasa.

Ta jaddada cewa za a magance matsalar bautar da yara, wadda ta ce talauci da rashin samun kariya ne kan gaba wajen haifar da su.

Kwanturola na ma’aikatar kwadago da inganta aiki ta kasa ta Jihar Neja, Hauwa Zakariyya, ta ce, “samar da tsaro da kiwon lafiya hakki ne a kan kowa, kuma ba za a samu wata ci gaba ba tare da tsaro ba.

“Shi ya sa muke daukar wannan kungiya ta ACCEL Africa da muhimmanci, saboda ta mayar da hankali kan wuraren haķar ma’adanai, domin daile aukuwar irin irin abin da ya faru a yankin Kuchiko, inda aka rasa rayuka da dama ciki har da yara kanana. Mun yi imanin cewar wannan tsari zai ilimantar da masu hakar ma’adanai yadda za su kare kansu a nan gaba.”

A nasa bangaren, kwantorulan na ma’aikatar kwadago na Jihar Osun, Solomon Ayinde Alabi, ya ce, “Muna murna da samun rahoto da ke tabbatar da cewa ficewar yara daga makarantu ya ragu sosai. Wannan babban labari ne gare mu a irin wadannan yankuna”.

“Ina kira gare mu a matsayinmu na iyaye  masu kulawa, da al’umma da mu yi amfani da wannan dama da kyau wajen kara azama wajen yaki da ta’addanci, bautar da yara a yankunanmu.”

Mahalarta taron sun ziyarci wuraren haķar ma’adanai a jihohi mabambata don gano hadarin da ke tattare da wannan aiki. Wani dan shekaraa Lawali Yusuf daga cikin masu haķar ma’adanai a Korokwa da ke Minna na jihar Neja ya ce, “ina wannan aiki ne saboda iyayena ba su da karfin daukar nauyin karatuna, shi ya sa nake yi don na tara kudi na fara zuwa makaranta kamar sauran abokaina.”

A yankin Idoka da ke Osun, wani dan shekara 11, Ibrahim da ke hakar ma’adanai ya ce, “burina shi ne zama mai hakar ma’adanai idan na girma, don haka ne ma na zo nan a matsayin yaron gida. Ina so na koyi yadda ake hako zinari duk da ma dai sau da dama ana kora ta daga wurin, sai dai ina dawowa saboda muradina ke nan zama mai haķar ma’adanai.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: bauatar da kananan yara hakar ma adainai yara bautar da yara a haķar ma adanai hakar ma adanai kawo karshen

এছাড়াও পড়ুন:

Nigeria: Zazzabin “Lassa” Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 118 Tun Farkon Wannan Shekara

Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025.

A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a cikin jahoji 33 na fadin kasar, kuma bincike da aka yi akan wadanda ake tsammanin ta kama, ya tabbatar da cewa an sami mutane 645 da su ka kamu da ita.

Ita dai wannan cutar mai yaduwa a Nigeria, ana kamuwa da ita ne ta hanyar cudanya a tsakanin mutane ko kuma taba kayan gida da su ka gurbana daga bahaya ko fitsari na mutane da su ka kamu da ita.

Tare da cewa an dauki shekara da shekaru ana fama da wannan cutar a cikin kasar ta Nigeria, sai dai har yanzu babu wani ci gaba na azo a gani da aka samu na dakile wannan cuta, saboda halayyar kazanta da rashin muhalli mai tsafta.

Ana samu wadanda suke tsira daga cutar amma a lokaci daya tana kisa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi
  • Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa
  • Obasanjo Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 700 A Kamaru
  • Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF
  • Wang Yi Ya Jinjina Wa Gudummawar Da Sinawa Da ’Yan Rasha Suka Bayar A Yakin Duniya Na Biyu
  • Nigeria: Zazzabin “Lassa” Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 118 Tun Farkon Wannan Shekara
  • DG VON Yayi Kira Ga Zaman Lafiya Da Hadin Kai Don Fadada Ci gaban Tattalin Arziki Da Ci Gaba.
  • Sin Ta Gano Babban Yankin Hakar Danyen Mai A Tekun Kudancin Kasar
  • Yawan Kayayyakin Da Aka Yi Hada-hadarsu A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Sin A 2024 Ya Ci Gaba Da Kasancewa Na Farko A Duniya
  • Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Kasashen Yamma Sune Yan Ta’adda Na Gasliya A Yankin