Masar : Za’a Gabatar Da Shirin Baiwa Falasdinawa Yancin Zama A Kasarsu
Published: 3rd, March 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya ce shirin sake gina Gaza wanda ya baiwa Falasdinawa yancin ci gaba da zama a kasarsu, za a gabatar da shi a taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a wannan mako.
Abdelatty a wani taron manema labarai a ranar Lahadin nan ya jaddada cewa shirin sake gina ba zai kasance na Masar ne kawai ko kuma na Larabawa ba amma zai nemi goyon bayan kasa da kasa don tabbatar da aiwatar da shi cikin nasara.
Abdelatty ya ce “Za mu yi tattaunawa mai zurfi tare da manyan kasashe masu ba da taimako da zarar an amince da shirin a taron kasashen Larabawa mai zuwa.”
Abdelatty ya ce bayan taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a ranar 4 ga Maris, za a yi taron ministocin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC cikin gaggawa, inda ministocin harkokin wajen kasashen waje za su matsa kaimi wajen gabatar da sakamakon taron a duniya.
Abdelatty ya kara da cewa “Za mu tabbatar da cewa an gabatar da sakamakon taron kasashen Larabawa ga duniya yadda ya kamata.”
Taron dai na da nasaba ne da shawarar da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar na kwace zirin gaza dama tilasta wa Falasdinawa barin Zirin su koma Jordan da Masar.
Trump Ya bayyana shirin ne yayin wani taron manema labarai a fadar White House a farkon watan Fabrairu tare da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya ziyarci Amurka.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasashen Larabawa Abdelatty ya
এছাড়াও পড়ুন:
Sani Ahmad Lere Na Radio Nijeriya Kaduna Ya Zama Falakin Lere
Mai martaba Sarkin Lere dake Kaduna Alhaji Sulaiman Umaru ya amince da nadin Sani Ahmed Lere Sardaunan Matasa zuwa Falakin Lere.
Hakan na kunshe ne a cikin takardar nadin da Sakataren Majalisar kuma Sadaukin Lere Alhaji Muhammad Lawal Ahmed ya sanya wa hannu.
Alhaji Muhammad Lawal Ahmed yace sabon nadin ya fara aiki ne nan take.
Ya bayyana cewa nadin Sani Ahmed Lere a matsayin Falakin Lere daga matsayinsa ne daga Sardaunan Matasan Lere wakilin Matasa a Masarautar zuwa Falakin Lere dan Majalisar Sarki kuma PPS ga Sarki.