An sake naɗa Obasa Kakakin Majalisar Legas
Published: 3rd, March 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus.
Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda.
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a AbujaBayan murabus ɗin nata, nan take ’yan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Nijeriya.
’Yan majalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayin mace ta farko kakakin majalisa.
Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ’yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar game da yadda za a shawo kan rikicin.
Mojisola Meranda dai ta yi murabus daga muƙamin ne bayan shafe kwanaki 49 tana mulki.
Meranda ta hau kujerar kakakin majalisar ne bayan da ’yan majalisar suka tsige Mudashiru Obasa a ranar 13 ga watan Janairu.
Meranda, wacce ta jagoranci zamanta na ƙarshe a yau Litinin, ta sha yabo da jinjina.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Legas Mojisola Meranda
এছাড়াও পড়ুন:
Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi
Ana tuhumar wata ma’aikaciyar kamfanin masaka a Jihar Goias ta ƙasar Brazil da laifin saka wa abokan aikinta guba bayan ta yi jayayya da su a kan abin da matar ta kira da rashin adalci wajen ƙarin matsayi da kamfanin ya yi.
Lamarin ya faru ne a wata masana’anta da ke Abadia de Goias, wani gari a yankin Goiânia Metropolitan.
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal Iran ta mayar wa Amurka martani kan barazanar kai mata hari’Yan sanda sun yi iƙirarin cewa, kyamarar daukar hoto cikin sirri (CCTV) ta kama wadda ake zargin mai shekara 38 tana buɗe wasu gorunan abin sha, wanda daga bisani wata ma’aikaciya ta sha, inda ta ji wani zafi a makogwaronta.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa, an sami wani nau’in ɗanɗano mai ƙarfi a cikin ruwan, wanda ke nuna cewa, wacce ake zargi da laifin tana son zuba wa abokan aikinta guba.
Shaidu sun bayyana cewa, matan biyu abokan juna ne, amma dangantakarsu ta yi tsami bayan ɗaya daga ciki ta samu ƙarin girma, wanda bai yi wa wadda ake zargi da laifin daɗi ba.
Sun yi ta jayayya, wanda ake zargin lamarin ya kai ga matakin zuba gubar.
’Yan sandan yankin sun shaida wa manema labarai cewa, wanda ake zargin mai shekara 38, ta kuma shiga ɓangaren da ake ajiye sinadarai na kamfanin, ba tare da izini ba.
An yi imanin cewa, ta haka ne aka gano ta yi amfanin da sinadaran a matsayin guba.
Bayan ɗaya daga cikin ma’aikatan ta sha, ta gano cewa akwai matsala, inda ta kira motar ɗaukar marasa lafiya, aka garzaya da ita asibiti domin duba ta, amma ta warke sarai, sai dai likitoci sun ce, an yi yunƙurin kashe ta.
‘Yan sanda sun kama wadda ake zargin a ranar 27 ga Fabrairu, bayan sun duba kyamarori na CCTV don gano abin da ake zargin ta, kuma ta amince da gurbata abin shan ga abokan aikinta bayan sun yi wata jayayya.
Mai yiwuwa za a tuhume ta da laifin yunƙurin kisan kai, wanda ke da hukuncin ɗaurin shekar 6 zuwa 20 a gidan yari.