Liu Jieyi: CPPCC Ta Aiwatar Da Shawarwari Sama Da 5000 A Cikin Shekarar Da Ta Gabata
Published: 3rd, March 2025 GMT
Da yammacin yau Litinin ne aka gudanar da taron manema labarai na taro na uku, na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC karo na 14, inda mai magana da yawun taron Liu Jieyi, ya gabatar da yanayin taron ga kafofin watsa labarai na kasar Sin da na waje, tare da amsa tambayoyin manema labarai.
A fannin gudanar da ayyuka da ba da shawarwari, Liu Jieyi ya gabatar da cewa, CPPCC ta mai da hankali kan batutuwa masu muhimmanci da wahala, da suka hada da inganta zamanantarwa irin ta Sin, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na zamantakewar al’umma, kuma ta gudanar da ayyuka da suka shafi tattauna batutuwan siyasa guda 85, da aiwatar da shawarwari sama da 5000, da kuma gabatar da bayanai sama da dubu 10.
CMG Zai Watsa Bikin Bude Zama Na Uku Na Majalisar CPPCC Karo Na 14 Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar NijeriyaYa ce kowane kwamiti na musamman na majalisar ya yi amfani da karfinsa don tsara aikin shigar mambobi sassan kauyuka, da masana’antu, da makarantu, da unguwannin birane, don tattara ra’ayoyi da shawarwari daga kowane bangare, wadanda suka ba da hidimomi ga jam’iyya da gwamnati, wajen aiwatar da manufofin siyasa, wanda hakan ya nuna muhimmiyar rawar da CPPCC ke takawa a cikin tsarin mulkin kasa.
Yayin da aka ambato halin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki, Liu Jieyi ya ce, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba mai inganci a shekarar 2024, inda GDPn kasar ya zarce yuan triliyan 134, kuma saurin karuwarsa ya kai 5%, wanda ya kasance a sahun gaba cikin manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Kaddamar Da Taro Na 10 Na Zaunannen Kwamitin Majalisar CPPCC Karo Na 14
An kaddamar da taro na 10 na zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a yau 1 ga watan Maris a nan birnin Beijing, inda memban hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban majalisar CPPCC Wang Huning ya halarci taron.
A gun taron, an zartas da kudurin gudanar da zama na 3 na majalisar CPPCC karo na 14 a ranar 4 ga wannan wata a birnin Beijing, an kuma gabatar da shawara kan ajendar zaman, wato sauraro da yin bincike kan rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar CPPCC da yadda aka gudanar da ayyukan da aka cimma daidaito a kai, a gun zama na 2 na majalisar CPPCC karo na 14, da halartar zama na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, da kuma sauraro da tattaunawa kan aikin gwamnatin kasar da sauran rahotanni. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp