NDLEA ta cafke madugun fataucin miyagun ƙwayoyi bayan shekaru 17 yana ɓuya
Published: 3rd, March 2025 GMT
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin madugun fataucin ƙwayoyi ne, Ogbonnaya Kevin Jeff, a maɓoyarsa da ke Jihar Legas.
Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Baba Femi, ya fitar ta ce kamen mutumin mai shekaru 59 na zuwa ne bayan shafe shekaru 17 yana ɓuya, inda yake fataucin miyagun ƙwayoyi na biliyoyin nairori a faɗin duniya.
Sanarwar ta ambato Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya yana bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja a yau Litinin.
Shugaban NDLEA ya kuma bayyana yadda jami’an sashen ayyukan musamman na hukumar suka riƙa bin diddigin Ogbonnaya biyo bayan nemansa ruwa a jallo da hukumar ’yan sandan duniya INTERPOL ke yi da kuma bayanan sirrin da hukumar leƙen asirin Koriya ta Kudu ta samar a kansa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fataucin ƙwayoyi Jihar Legas Ogbonnaya Kevin Jeff
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda yake ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki a Kano.
Alhaji Sunusi, ya rasu yana da shekaru 92 bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin MusulunciYa rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama, ciki har da Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora nagari da ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin gargajiya.
Ya ce gudunmawar da ya bayar za a ci gaba da tunawa da ita ba kawai a Kano ba, har ma da Najeriya baki ɗaya.
Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Jihar Kano, Majalisar Masarautar Kano, da iyalan mamacin.
Ya kuma yi addu’a Allah ya jiƙansa da rahama, ya kuma sanya Aljanna Firdausi ta zama makoma a gare shi.