Dalilin da ba za mu binciki Akpabio kan zargin cin zarafin Natasha ba — Majalisar Dattawa
Published: 4th, March 2025 GMT
Majalisar Dattawa ta sanar da cewa a halin yanzu ba ta da hurumin gudanar da bincike kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduagha ke yi wa Sanata Godswill Akpabio.
A bayan nan dai ana ci gaba da samun ƙarin kiraye-kirayen gudanar da cikakken bincike kan zargin da Sanata Natasha ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio a kan cewar ta ƙi ba shi haɗin kai, shi ne ya sa ya ke yi mata bita da ƙulli.
Sanata Natasha Akpoti Uduaghan daga Jihar Kogi ta yi wannan zargin ne jim kaɗan bayan da aka soma kai ruwa rana tsakaninta da Sanata Akpabio, lamarin da ya sa a yanzu Majalisar Dattawan ke binciken Sanata Natasha bisa zargin nuna rashin ɗa’a.
Ita dai Sanata Natasha ta nuna tirjiya bayan da aka sauya mata wurin zama a zauren Majalisar Dattawa inda ta yi zargin cewa matakin na da nufin rufe mata baki tare da kawo mata cikas wajen gudanar da aikinta.
Saboda irin ƙurar da ta tayar sai Majalisar ta yanke shawarar cewa Sanatar ta bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa domin ta kare kanta.
Sai dai kafin ta bayyana a gaban kwamitin, Sanata Natasha a wata hira da gidan talibijin na Arise, ta yi zargin cewa shugaban majalisar Akpabio ya nemi ya yi lalata da ita kuma ba ta ba shi haɗin kai ba, shi ne abin da ya janyo ya sa mata ƙahon zuƙa har aka sauya mata wurin zama.
Sanata Natasha ta kuma maka shugaban Majalisar Dattawan a gaban kuliya inda take neman diyyar Naira biliyan 100 saboda zargin ɓata mata suna.
Dalilin da ba za mu binciki Akpabio ba — Majalisar DattawaSai a wata hira da gidan Talabijin na Arise a ranar Litinin, Shugaban Kwamitin Hulɗa da Jama’a na Majalisar Dattawan, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce ba za su iya bincikar Sanata Akpabio saboda har kawo yanzu Sanata Natasha da ke zarginsa da cin zarafi ba ta shigar da wani ƙorafi a hukumance ba.
Sanata Adaramodu na jam’iyyar APC daga Jihar Ekiti ya ce babu wani ƙorafi da Sanata Natasha ta shigar a gaban kwamitin ɗa’a da ladabtarwa ko kwamitin karɓar ƙorafi ballantana a gudanar da bincike a kan lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: cin zarafi Majalisar Dattawa Majalisar Dattawan Majalisar Dattawa gaban kwamitin
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 7 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Fyaɗe Da Kashe Budurwa A Bauchi
An garzaya da ita asibitin Misau, daga nan aka mayar da ita zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare, inda aka tabbatar da mutuwarta.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis.
Ya ce waɗanda aka kama sun amsa laifin kuma sun bayyana sunayen wasu da suka haɗa kai da su.
Cikin sauran waɗanda aka kama har da Alkali Kawu, Maule Mai Ride, Mai Tumatir, Danguli, Yakubu da Kura.
Wakil ya ce bincike yana guduna a hedikwatar ‘yansanda ta Misau, kuma sun ƙudiri aniyar ganin adalci ya tabbata.
Ya ƙara da cewa bayan kammala bincike, za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci daidai da laifin da suka aikata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp