An Fara Haska Fim Din Sin A Sinimomin Najeriya Da Ghana Da Laberiya
Published: 4th, March 2025 GMT
A ranar 28 ga watan Fabarairun da ya shude ne aka saki wani fim din kasar Sin mai lakabin “Creation of the Gods II: Demon Force”, a gidajen kallon sinima 39 dake sassan tarayyar Najeriya, da kuma wasu 2 dake kasar Ghana, da sinima 1 a Laberiya.
Wannan ne dai karon farko da aka saki wani fim da aka shirya a kasar Sin kai tsaye, a allunan sinima na kasashen yammacin Afirka.
Ana sa ran ci gaba da haska wannan fim har zuwa ranar 6 ga watan nan na Maris. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tun bayan kisan mafarauta 16 da ke hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu.
A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken ‘yanci, suna da damar kutsawa lungu da saƙo na ko’ina a fadin kasar nan, wasu kuwa tambaya suke shin me ya kai ‘yan Arewa har kudancin kasar nan don yin farauta?
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin SallahShirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa mafarautan arewa zuwa kudancin Najeriya yin farauta.
Domin sauke shirin, latsa nan