Jami’an tsaro sun hana jama’a kwasar mai bayan hatsarin tanka a Taraba
Published: 4th, March 2025 GMT
Jami’an tsaro sun hana mutane zuwa kwasar man fetur daga wata tankar mai da ta yi hatsari a Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba.
A safiyar ranar Litinin ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), suka ɗauki wannan mataki bayan faɗuwar tankar man a kan babban hanyar Jalingo zuwa Wukari.
Rahotanni sun bayyana cewa faɗuwar tankar man ke da wuya, jami’an tsaron suka isa wurin, inda suka killace wurin domin hana mutane kaiwa inda man yake.
Daga nan ɗauke tankar man da babbar motar ɗauko, aka mayar wata motar sannan aka tafi da ita.
NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba NDLEA ta cafke madugun fataucin miyagun ƙwayoyi bayan shekaru 17 yana ɓuyaKakakin Hukumar NSCDC ne jihar, SC Sam Illiya, ya bayyana wa wakilinmu cewa kwamandan hukumar na jihar da kansa ya jagoranci jami’ansa zuwa wurin domin gudanar da aikin.
Kakakinn ’yan sanda na jihar, SP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jami an Tsaro Kwasar man fetur Tankar
এছাড়াও পড়ুন:
An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu a Kudu
An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP).
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito ne daga ƙauyen Minda da ke Ƙaramar hukumar Lau a Jihar Taraba.
Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52 Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a BornoA yayin da take zantawa da manema labarai a Jalingo, ranar Juma’a ta ce an yaudari yaran daga unguwar su aka yi safarar su zuwa jihohin Kudu maso Gabas.
Ta ce, sun gano su kuma sun ceto su a garin Aba, a Onitsha da kuma wani ɓangare na Jihar Imo tare da iƙirarin waɗanda suka yi safarar su da cewa su marayu ne.
Ta bayyana cewa, an damƙe masu aikata safarar ne a garin Gembu da ke ƙaramar hukumar Sardauna, a lokacin da suke gudanar da haramtattun aikinsu, wanda ya kai ga ceto yaran takwas, yayin da wasu da dama da aka yi safarar su ba a kai ga ceto su ba.
Waɗanda aka yi safarar ta su a ƙarshe sun sake haɗuwa da iyayensu a watan Maris 2025, sun tabbatar da cewa an sayar da su ba tare da sanin iyayen su ba.
“Bayan ɗaukar matakin gaggawa da ma’aikatar ta yi da kuma Hukumar NAPTIP, an dawo da takwas daga cikin yaran Jihar Taraba cikin lafiya.