Bidiyon batsa: Kotu ta ɗaure ’yan Tiktok biyu a Kano
Published: 4th, March 2025 GMT
Bidiyon batsa ya ja wa wasu ’yan Tiktok biyu hukuncin ɗaurin shekara guda kowannensu a gidan yari bayan an gurfanar da su gaban kotu a Jihar Kano.
Kotun Majiatare da ke Norman’s Land a Ƙaramar Hukumar Fagge ta yanke wasu ’yan Tiktok din hukunci ne bayan samun su da laifin saɓa wa dokokin Musulunci da kuma tsarin zamantakewar al’ummar jihar.
’Yan TikTok ɗin da suka haɗa da Ahmad Isa da Maryam Musa waɗanda dukansu ’yan unguwar Ladanai ne da ke yankin Hotoro ne.
Sun gurfana a kotu ne bayan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta cika hannunta da su.
Jami’an tsaro sun hana jama’a kwasar mai bayan hatsarin tanka a Taraba Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok bayan Hisbah ta daina kamensu NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ BaLauyan Gwamantin Kano, Barista Garzali Maigari Bichi, ya karanta wa matasan takardar tuhumar da ake musu na haɗa baki tare da yaɗa bidiyon da bai dace ba a dandalin sada zumunta, kuma sun amsa laifin.
Daga nan alƙalin kotun, Mai Shari’a Hadiza Muhammad Hassan ta yanke wa kowannensu hukuncin zaman shekara guda a gidan yari.
Ta kuma ba su zaɓin biyan tarar Naira dubu ɗari kowannensu, tare da gargaɗin su da su zama mutanen kirki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan TikTok
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki domin tallafa wa mabuƙata a wannan wata mai albarka na Ramadana.
Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya ƙaddamar da rabon abincin a cibiyar Dandali da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a jihar.
HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarkiBayanai sun ce gwamnatin jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta ƙaddamar da wannan shiri tana da burin raba abincin buɗa-baki ga mabuƙata masu azumtar watan Ramadana.
Gwamnatin ta ce an tanadi cibiyoyi 91 domin raba wa mabuƙata 91,000 abincin buɗa-baki duk rana nan da tsawon kwanaki 27 masu zuwa.
Domin tabbatar da samun nasara, gwamnatin ta ce ta ɗauki masu aikin girke-girke da za su riƙa dafawa sannan su raba wa mabuƙata abincin.
Mataimakin Gwamnan wanda shi ne ke jagorantar shirin raba abincin a bana, ya bayyana gamsuwarsa da yadda aka ƙaddamar da shirin, yana mai kiran waɗanda aka ɗora wa alhakin aikin su tabbatar da raba wa mabuƙata abincin a kan kari.
Aminiya ta ruwaito cewa, Mataimakin Gwamnan ya samu rakiyar wasu ƙusoshin Gwamnatin Kano wajen ƙaddamar da rabon abincin da suka haɗa da Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya da Kwamishinan Harkokin Addini, Sheikh Tijjani Auwal da sauransu.
Gwamnatin Kano ta jaddada ƙudirinta na rage raɗaɗin al’umma musamman Musulmi a wannan wata mai falala.