Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta MDD Ta Ce Sauye-Sauyen Da Ke Faruwa A Amurka Zai Shafi Al-Amura Da Dama A Majalisar
Published: 4th, March 2025 GMT
Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta bada sanarwan cewa, sauye –sauye na asasi dake faruwa a kasar Amurka, zai shafi hukumar da ma MDD.
Kwamishinan hukumar Volker Turk ya bayyana cewa fadar ‘White House’ a halin yanzu ta na gudanar da sauye-sauye na asasi a cikin hukumomi da ma’aikatu a Amurka, wadanda kuma za su shafi al-amura da dama a cikin gida da kuma sauran kasashen duniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan majalisar dokokin Aljeriya sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila
‘Yan majalisar dokokin Aljeriya, sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila.
‘Yan majalisar dokokin Aljeriya da wakilan jama’a na kasar a zaman majalisar dokokin kasar, sun yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila ke aikatawa akan al’ummar Gaza, tare da nuna cikakken goyan bayansu ga falasdinawa.
Mahalarta taron sun yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta yi amfani da dokar da ta haramta daidaita alaka da gwamnatin mamayar Isra’ila.
Mustapha Yahi, sakatare-janar na National Democratic Rally (RND) ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da wakilin jaridar Al-Alam: inda yake cewa “Mun sake yin Allah wadai da ci gaba da ta’addancin isra’ila.
Abdelaali Hassani Cherif, shugaban kungiyar Movement of Society for Peace (MSP), ya jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa na cikin gida don tinkarar zaluncin da kasashen yammaci da wasu kasashe ke yi a yankin t ahnayar goyon bayan matsayar Aljeriya kan batun Falasdinu.
Kusan shekaru uku da suka gabata, a cikin 2022, ‘yan majalisar dokokin Aljeriya sun kirkiro wani shiri na haramta duk wani yunkuri ko shiri na daidaitawa da Isra’ila.