OPEC Da Kawayenta Zasu Kara Yawan Man Da Suke Haka A Karon Farko Tun Shekara Ta 2022
Published: 4th, March 2025 GMT
A wani rahoto wanda ba’a tantance ba kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta a wajen kungiyar OPEC + za su kara yawan man fetur da suke haka da ganga 138,000 a cikin watan Afrilu mai zuwa.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wasu majiyoyin kungiyar wadanda ba’a bayyana ba suna cewa kungiyar OPEC + bata kara yawan man da take haka ba na lokaci mai tsawo, amma a halin yanzu zata kara kamar yadda aka sanar.
Labarin ya kara da cewa kungiyar tana rage ganga miliyon 5.85 wanda kuma shi ne kashi 5.7% na yawan man da ake haka a duniya, wannan kuma ya yi dai dai da shawarar da OPEC + suka dauka tun shekara ta 2022.
Labarin ya kara da cewa kasashen kungiyar sun amince da haka daga ciki har da kasar Rasha kasar da ta fi ko wace kasa hakar mai a duniya.
Akwai jitajitan cewa Amurka zata kara takurawa Iran a cikin watanni masu zuwa, amma Iran ta ce hakan ba zai shafi ta ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Haddiyar Daular Larabawa Sun Gudanar Da Taron Kwamitin Siyasa Da Al-adu Na Kasashen Biyu
Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin kasashe makobta na daga cikin manufofin JMI ta harkokin wakashen waje.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa karfafa dangantaka da Hadaddiyar Daular Larabawa yana daga cikin manufofin JMI don biyan bukatun ko wace kasa daga cikin kasashen biyu.
Ya kuma kara da cewa akwai bukatar kasashen musulmi su kara hadin kai a tsakaninsu don magance matsalar da Falasdinawa suke fuskanta a hannun HKI da kuma kasashen yamma.