Miji ya yi yunƙurin kashe matarsa kan zargin maita
Published: 4th, March 2025 GMT
Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari kan zargin barazana ga rayuwar matarsa da yake zargin ta da maita.
Babbar Kotun Musulunci da ke Gazawa a Jihar Kano ta tsare mutumin ne bayan ya yi barazana tare da yunƙurin kai wa matar tasa farmaki da adda.
Mai gabatar da ƙara, Sadiq Yusuf ya shaida wa kotun cewa mutumin ya yi yunƙurin aika-aikan ne bisa zargin matarsa da kama kuruwar ɗansu da ya jima yana fama da rashin lafiya.
Magidancin da ke zaune a ƙauyen Gawo da iyalin nasa ya musanta tuhumar da ake masa, don haka, Alƙali Nura Ahmad ya ba da umarnin tsare shi a gidan yari.
Bidiyon batsa: Kotu ta ɗaure ’yan Tiktok a gidan yari a Kano NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ BaYa kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 20 ga watan nan na Maris domin masu ƙara su gabatar da shaidu.
Ɓari: Matan aure sun yi wa wata barazanaA wata sabuwa kuma, an gurfanar da wasu matan aure biyu kan zargin yin barazana ga wata da suke zargi da haddasa zubewar juna biyun dayarsu.
Kotun da ke zamanta a unguwar Danbare, Ƙaramar Hukumar Kumbotso, na zargin matan auren da haɗa baki da yunƙurin aikata laifi.
Ana zargin matan waɗanda mazauna unguwar Rimin Auzinawa da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo da barazanar ga matar tare da zargin ta da haddasa zubewar juna biyun dayarsu.
Sai dai sun musanta zargin, inda daga baya alƙalin, Khadi Munzali Idris Gwadabe, ya ba da belinsu, bayan lura da yanayin lafiyar wadda ta yi ɓarin, da ke murmurewa.
Ya kuma daga sauraron shari’ar zuwa ranar 16 watan Afrilu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɓarayin waya a Kano
Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago.
Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar SakkwatoSai dai kakakin ’yan sandan ya ce wani abokin ɓarawon da suka yi yunƙurin aika-aikar tare ya tsere da wayar da suka sata.
SP Kiyawa ya ce bayan binciken da aka gudanar ne ’yan sanda suka cafke wani mai suna Abduljabbar Musa Sheka kan zargin sayen wayoyin hannu da aka sata.
Ya ƙara da cewa za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar sun kammala bincike.
Rundunar ta gargaɗi ’yan kasuwa da su zama masu lura da abokan hulɗar da suke mu’amala da su, yana mai cewa akan samu miyagu da suke sojan gona a matsayin masu sayen kayayyaki a kasuwa.
Kazalika, rundunar ta yi kira ga duk wani ɗan kasuwa da irin haka ta faru da shi da ya gaggauta kai rahoto ofishin ’yan sanda mafi kusa.