Trump Ya Dakatar Da Taimakon Da Kasarsa Take Bai Wa Ukiraniya
Published: 4th, March 2025 GMT
Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna a halin yanzu sun isa kasar Poland.
Jaridar “Bloomberg” ta bayyana cewa; bayan kwanaki kadan da aka yi cacar baki a tsakanin shugaban na Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na Ukiraniya Volodymyr Zelensky, shugaban na kasar Amurka ya bayar da umarnin a dakatar da bai wa Ukiraniya duk wani taimako na soja.
Wani jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa; “ Amurkan ta dakatar da duk wani taimako na soja da take bai wa Ukiraniya a halin yanzu, har zuwa lokacin da shugabannin kasar za su nuna cewa da gaske suna son zaman lafiya.”
Ita kuwa jaridar “Washington Post” ta nakalto cewa, jami’an gwamnatin Amurkan suna kuma nazarin yadda za su dakatar da musayar bayanai da suke yi da Ukiraniya, haka nan horon soja da ake ba su.”
A ranar juma’ar da ta gabata ne dai shugaban kasar Ukiraniya Volodymyr Zelensky ya kai ziyara Amurka, sai dai ba ta kare da dadi ba a tsakaninsa da shugaban kasar Donald Trump, saboda sabanin da su ka samu akan batun tsagaita wutar yaki da kuma yarjejeniya akan ma’adanai.
Trump ya zargi shugaban na Ukiraniya da kokarin kunna wutar yakin duniya na 3,alhali bai taki wani abu ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Masar ta ki amincewa da duk wani yunkuri na kafa gwamnatin ‘yan adawa a Sudan
Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar Larabawa ta Masar ta yi watsi da duk wani mataki da ke kawo barazana ga hadin kan Sudan, ciki har da yunkurin kafa gwamnatin ‘yan adawa, saboda hakan zai kara dagula al’amuran siyasa da kuma kawo cikas ga kokarin hada kan kasar.
Alkahira ta bukaci dukkan bangarorin da su yi aiki mai inganci tare da cikakken tsari na siyasa, da nufin cimma daidaito da kuma maido da tsaro a fadin kasar.
Ta kara da cewa, “Masar ta bukaci dukkan sojojin Sudan da su ba da fifiko ga cin moriyar kasa mafi girma da kuma taka rawar gani wajen bullo da wani cikakken tsari da zai kawo hadin da daidaito ba tare da nuna banbanci ko tsoma bakin kasashen waje ba.”
Ministan harkokin wajen Sudan Ali Youssef al-Sharif ya tabbatar a karshen watan da ya gabata cewa “babu wanda zai amince da abin da ake kira gwamnatin hadaka a Sudan, kuma babu wata kasa da za ta amince da ita.