Syria: Sojojin HKI Sun Kai Wa Yankin Tartus Hari
Published: 4th, March 2025 GMT
Kamfanin dillancin labarun “Sana” na kasar Syria ya ambaci cewa; jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a wani wuri dake gefen garin Tartus, sai dai babu rahoto akan asarar rayuka har yanzu.
Kamfanin dillancin labarun “ Sana” ya ci gaba da cewa; Ma’aikatan agaji suna kokarin gano hakikanin inda aka kai wa harin.
Su kuwa sojojin HKI sun sanar da kai hari ne akan wani rumbun makamai dake yankin “Kardaha’.
Wannan ba shi ne karon farko da sojojin na HKI su ka kai hari a garin Tartus ba, a ranar 16 ga watan Disamba ba sun kai wannan irin harin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gobara ta lalata wani ɓangare na gidan Ado Bayero
Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Alhamis ta lalata wani sashe na shahararren gidan Ado Bayero da ke ƙofar Nassarawa a Kano.
Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a hawa na tara na ginin da cibiyar Jami’ar Northwest University take.
Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a FilatoRahoton na cewa gobarar ta shafi wani sashe na sashen ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa na jami’ar.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’an kashe gobara amma abin ya ci tura domin an kasa samun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ta wayar salula zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.