Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin sakataren kwamitin wanda dama shi ne mataimakin darakta na hanyoyin ruwa na cikin gida a wannan ma’aikata.

Ministan ma’aikatar tattalin arziki na ruwa, Adegboyega Oyetola ne ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki tukuru domin  kare hatsurran kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a cikin kasar.

Ministan da yake Magana a wurin kaddamar da wannan kwamitin a birnin Abuja, ya yi kira da a yi aiki tukuru domin magance yawan hatsurran da ake samu na  jiragen ruwa a cikin gida wanda yake haddasa asarar rayuka da dama.

A Nigeria dai ana yawan samun hatsarin kananan jiragen ruwa masu jigilar mutane musamman ma dai a cikin arewacin kasar, da hakan yake haddasa asarar rayuka da yawa. Cunkoson mutanen da suke hawa knanan jiragen da kuma rashin rigunan tsira idan hatsari ya faru, suna cikin dalilin asarar rayuwa masu yawa da ake samu. Haka nan kuma karancin masu ceto mutane da za su zama aikinsu kenan a gabar ruwa, idan aka sami bullar hatsurra.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kasar Sin Ta Caccaki Matakin Kakaba Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Da Amurka Ta Dauka, Ta Kuma Sha Alwashin Kare Moriyarta

Ta kuma bukaci Amurka da ta daina amfani da harajin fito a matsayin makami don dakile ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, da kuma tauye hakkin samun halaltacciyar ci gaba na al’ummar Sinawa. (Mohammed Yahaya)

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dangantaka ta yi tsami tsakanin Aljeriya da kasashen kawancen Sahel
  •  HKI Ta Kai Munanan Hare-hare Akan Yankin Khan-Yunus
  • Arakci: Amruka Tana Mafarkin Kulla Yarjejeniya Da Iran Kwatankwanci Wacce Ta Yi Da Kasar Libya
  • Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 30 a Kongo
  • Hanyoyin Warware Matsalolin Ma’aurata(1)
  • Ana Ci Gaba Da Kai Ruwa Rana Takanin Amurka Da China Kan Batun Harajin Fito
  • Finafinan Kannywood da suke tashe da kuma manyan marubutansu
  • Ba Rabo Da Gwani Ba: Abdullahi Karkuzu 1931-2025
  • Gwamnatin Kasar Sin Ta Caccaki Matakin Kakaba Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Da Amurka Ta Dauka, Ta Kuma Sha Alwashin Kare Moriyarta
  • Francesca Albanze: Abinda Yake Faruwa A Gaza Kisan Kiyashi Ne