Gidauniyar Sir Ahmadu Bello Ta Yi Kira Ga Hadin Kai Da Adalci A Ramadan
Published: 4th, March 2025 GMT
Yayin da al’ummar Musulmai a Najeriya da duniya ke fara azumin watan Ramadan, Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta aike da sakon fatan alheri, tana kira da a yi amfani da wannan lokaci mai daraja wajen sabunta zukata da nuna tausayi da karfafa hadin kai a kasa.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Janar na gidauniyar, Abubakar Gambo Umar ya sanya wa hannu, ta jaddada bukatar kyautata dabi’u da wanzar da zaman lafiya da adalci a kasuwanci a lokacin azumi.
Gidauniyar ta yi kira ga malaman addini da su ci gaba da yada sakonnin tsoron Allah da hakuri da kaunar juna, domin karfafa darussan Ramadan na sabunta imani da hadin kan al’umma.
Hakazalika, gidauniyar ta gargadi ’yan kasuwa da dillalai da su guji tsawwala farashi da cutar da mabukata, tana mai cewa Ramadan lokaci ne na tausayi da taimakon juna, ba wahala da neman riba ta haram ba.
“Yayin da muke tsarkake kanmu ta hanyar azumi da ibada, mu kuma daga murya cikin addu’a don hadin kai, zaman lafiya, da ci gaban ƙasarmu ƙaunatacciya. Allah Ya baiwa shugabanninmu shiriya, Ya kuma ba ƙasarmu ƙarfin da za ta shawo kan ƙalubalen da take fuskanta. in ji sanarwar”.
Gidauniyar ta jaddada kudirinta na karfafa zaman lafiya da adalci da daidaito a cikin al’umma, tare da kira ga ’yan Najeriya da su rungumi kyawawan halaye na Ramadan—imani, hakuri da karamci.
A karshe, gidauniyar ta yi fatan Allah Ya albarkaci kowa da zaman lafiya da rahama a wannan wata mai alfarma.
Rel: Khadija Kubau
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gidauniyar Kira Ramadan
এছাড়াও পড়ুন:
Wike Ya Musanta Jita-jitar Faɗuwa Ta Rashin Lafiya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp