RAMADAN: Gwamnatin Jigawa Ta Rage Lokutan Aiki Ga Ma’aikatan Jihar
Published: 4th, March 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a Jihar Jigawa yayin azumin Ramadan na 2025.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar kuma aka rabawa manema labarai aDutse, wacce Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya sanya wa hannu.
“Farawa daga yanzu, ma’aikatan gwamnati a jihar za su rika fara aiki da karfe 9:00 na safe kuma su tashi da karfe 3:00 na yamma daga Litinin zuwa Alhamis, raguwar awanni biyu daga tsohon lokacin rufewa na karfe 5:00 na yamma.
Babban Sakataren ya bayyana cewa an yi hakan ne domin baiwa ma’aikatan gwamnati damar shiryawa azumin Ramadan da kuma gudanar da ibadu cikin sauki a wannan wata mai alfarma.
“An yi fatan cewa ma’aikatan gwamnati za su yi amfani da wannan lokaci don yin addu’o’i domin samun shiriya da albarka ga jiharmu,” in ji shi.
Alhaji Muhammad Dagaceri ya kara da cewa ana sa ran ma’aikatan za su yi amfani da lokacin azumi wajen yin addu’o’in zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki ga jihar da kasa baki daya.
END/ USMAN MZ
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ma aikatan Jihar Rage
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Bukaci A Ci Gaba Da Tallafawa Mabukata Bayan Ramadan.
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan.
Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara.
Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban kasar na ciyar da kasar gaba.
“A madadin ‘ya’yan jam’iyyar APC na Zamfara da al’ummar mazaba ta, na mika sakon taya murna ga shugaba Tinubu na cika shekaru 73 da haihuwa. “Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya kara masa shekaru masu yawa cikin koshin lafiya, da wadata, da kuma hikimar da zai jagoranci kasar nan ta hanyar da ta dace. Za mu ci gaba da yi masa addu’ar samun nasara a matsayinsa na shugaban kasa,” inji shi.
COV/AMINU DALHATU