Kasafin Kudin Bana Zai Samarda Tsarin Tattalin Arziki Da Cigaban Ƙasa: Ministan Labarai
Published: 4th, March 2025 GMT
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗin bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da Ministoci karo na uku da aka gudanar a Cibiyar Manema Labarai ta Ƙasa, Abuja, a yau.
Mohammed Idris ya jaddada cewa kasafin kuɗin wannan shekarar ya mayar da hankali kan zuba jari a sassa masu muhimmanci da ke da tasiri na kai tsaye kan jin daɗi da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
“Kasafin kuɗi na 2025 ba kawai wata takarda ta kuɗi ba ce; yana nuna tsari mai ƙarfi na daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa. Wannan kasafin ya maida hankali kan harkokin tsaro da ababen more rayuwa da ilimi da lafiya da ma’adinai da noma da wasu sassa masu matuƙar muhimmanci ga cigaban ƙasa.”
“Wannan shekara ta 2025, shekara ce ta tabbatar da sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Tinubu ta aiwatar, domin a fara jin ɗadin su a zahiri. Tuni muna gani a fili cewa farashin kayan abinci yana raguwa a hankali, wanda ke kawo sauƙi ga ‘yan ƙasa,” in ji shi.
Ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta tabbatar da aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata, tare da nuna gaskiya da riƙon amana wajen cimma burin shirin ”
“Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tuƙuru wajen aiwatar da wannan kasafin kuɗi domin cimma cikakken tasirinsa a rayuwar al’ummar mu. Don haka, ina kira ga duk ‘yan ƙasa su mara wa waɗannan ƙoƙari baya, domin mu gina Najeriya,” in ji shi.
Ministan ya yaba wa kafafen yaɗa labarai bisa jajircewarsu wajen kawo rahotanni kan taron, yana jaddada muhimmancinsu wajen yaɗa sahihan labarai da suka dace, ba tare da son rai ba, tare da mai da hankali kan ci gaban ƙasa.
Ya nanata cewa kafafen yaɗa labarai suna ba da gudunmuwa wajen tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya da kuma tabbatar da cewa ‘yan Najeriya na samun ingantattun bayanai kan manyan tsare-tsaren sauyi da gwamnati ke aiwatarwa.
Mohammed Idris ya bayyana cewa dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne ta hanyar tattaunawa bisa sani, fahimtar juna, da haɗin gwiwa don cigaban ƙasa. Saboda haka, ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da kiyaye ƙa’idodin daidaito, alhaki, da ƙwarewa a cikin rahotanninsu.
“A wannan zamani da labaran ƙarya da son rai ke iya rinjayar tunanin jama’a cikin sauƙi, sadaukarwarku ga gaskiya da adalci ya fi zama mai muhimmanci fiye da da. Dole ne mu yi aiki tare don tabbatar da cewa bayanan da ke tsara ra’ayoyin jama’a sun dace da ainihin gaskiyar yadda ake tafiyar da mulki, ba tare da son rai ko ƙayatarwa maras tushe ba,” in ji shi.
Taron Minista karo na uku ya kuma samu halartar Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, da Ministan kasa, Sanata John Owan Enoh.
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Arziki Ƙasa Minista Samarda Tsarin
এছাড়াও পড়ুন:
Angola Zata Shiga Shirin ‘Yankunan Kasuwanci’ Na Kungiyar SADC
Kasar Angola ta bada sanarwan cewa, zata shiga shirin kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC na yankunan kasuwanci, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen yankin .
Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa shigar Angola cikin tsarin yankunan kasuwanci, SADC kuma a matsayin mamba na 14 a wannan tsarin zai dauke kudin fito tsakanin kasashen 13 da Angolar. Wannan har’ila yau zai kara fadin kasuwar kasashen kungiyar ta SADC.
Labarin ya kara da cewa bayan tattaunawa mai tsawo daga karshe Angola ta sami amincewar mafi yawan kasashen kungiyar ta SADC mai mambobi 16.