Aminiya:
2025-03-04@14:45:00 GMT

Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki

Published: 4th, March 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage tsawon lokacin aikin ma’aikatanta nan take albarkacin watan Ramadan.

Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin ne domin ba wa ma’aikata damar samun hutut da kuma  gudanar da ibada a wannan wata mai albarka.

Shugaban Ma’aikata na jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya sanar da cewa ce daga yanzu lokacin aiki ya koma karfe 9 na safe zuwa 3 na yamma a ranakun Litinin zuwa Alhamis.

Sanarawar ta kara da cewa ranar Juma’a kuma za a rika tashi aiki karfe 1 na rana har zuwa karshen watan azumin.

Ya kuma yi kira ga ma’aikata da su yi amfani da watan ibadar wajen yin addu’o’in samun sauki a fannin tattalin arziki da zaman lafiya a Jihar Jigawa da ma kasa ba ki daya.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ramadan

এছাড়াও পড়ুন:

MDD ta taya Musulmi murnar zuwan watan Ramadan

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar watan Ramadan, yana mai bayyana wannan lokaci a matsayin mai cike da falala, tausayi, da zaman lafiya.

A sakon da MDD ta fitar ta hannunsa, Guterres ya ce, “Ramadan lokaci ne da ke karantar da kyawawan ɗabi’u na tausayawa, taimakekeniya, karamci, da mutunta juna. Wannan wata dama ce ta ƙara hada kai, sada zumunta, da gina al’umma mai cike da zaman lafiya.”

Ya kuma jaddada muhimmancin tunawa da waɗanda suke cikin hali na ƙunci, musamman ’yan gudun hijira da waɗanda ke fama da rikice-rikice a wurare kamar Gaza, Sudan, da yankunan Sahel.

Guterres ya bayyana damuwarsa kan halin da suke ciki, yana mai cewa, “Ina tare da ku a wannan lokaci mai albarka, kuma ina roƙon samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a gare ku.”

 

Ya yi kira ga al’umma da su yi amfani da wannan wata mai alfarma wajen haɗa kai da tabbatar da zaman lafiya.

“Zaman lafiya shi ne ginshiƙin rayuwa, kuma ya kamata mu yi aiki tare don gina duniya mai cike da adalci da mutunta juna,” in ji shi.

Sakatare Janar ɗin ya kuma bayyana cewa a kowanne Ramadan, yana yin azumi tare da al’ummar Musulmi a faɗin duniya, abin da ke ƙara masa fahimtar kyawawan dabi’u na Musulunci da kuma ƙwarin gwiwa.

A karshe, Guterres ya yi fatan Allah Ya karɓi ibadar al’ummar Musulmi yayin da suke azumtar wannan wata mai albarka, yana mai cewa, “Ina taya ku murnar wannan lokaci mai cike da albarka da tausayi.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • RAMADAN: Gwamnatin Jigawa Ta Rage Lokutan Aiki Ga Ma’aikatan Jihar 
  • Jami’an tsaro sun hana jama’a kwasar mai bayan hatsarin tanka a Taraba
  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Gargadi Malaman Da Ba Sa Zuwa Aiki
  • Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Shirin Ciyarwar Na Watan Ramadan
  • Masana Fasahar Gina Jiragen Sama A Iran Sun Samar Da Wata Fasahar Nano Mai Rage Nauyin Jiragen Sama
  • Ramadan: Coci ya ciyar da Musulmi 1,000 a Kaduna
  • MDD ta taya Musulmi murnar zuwan watan Ramadan
  • Hukumar NOA Ta Bukaci Al’umma Su Kara Hakuri Da Kaunar Juna
  • Babban Sakataren MDD Ya Taya Musulmi Murnar Shiga Watan Ramadan