Za’a yi Garambawul Kan Dokar Amfani Da Shafukan Sada Zumunta A Kasar Nijer
Published: 4th, March 2025 GMT
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bayyana aniyarta ta yin garambawul ga dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta irin su Whatsapp da Facebook da dai sauransu a kasar.
Ministan sadarwa na kasar Nijer sidi Mohammad Raliyu shi ne ya bayyana hakan, yana me cewa duk wani zaure na Whattsapp ko Facebook da ya kunshi mutanen 50 zuwa 100 dole ne yayi rajista a wajen hukuma don ci gaba da aikinsa.
Ministan ya ce zaurukan whattsap da Facebook na zama hanyoyin kasuwanci da kuma yaƙar gwamnatoci, wannan yasa za ta bullon da sabon shiri tare da wasu ƙasashen Afirka domin sake duba dokar da ta bada damar aiki da shafukan sada zumunta a Kasashen, domin dakile amfani da ita ta hanyar da bata dace ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Tsaron Pakistan Ya Yi Wa Pakistan Barazanar Kai Mata Hari Mai Tsanani
A daidai lokacin da sabani yake yin tsanani a tsakanin India da Pakistan, bayan wani hari da aka kai a Kashmir da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 26, ministan tsaron kasar Pakistan Khajah Asif ya ce; matukar India ta keta hurumin kasarsa, to kuwa za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani.
Minista Khajah Asif ya kuma gargadi kasar ta India da ta guji keta hurumin kasar Pakistan.
Asif ya kuma bukaci India da ta gudanar da bincike akan harin da aka yi a ranar Talata a yankin Kashmir, kuma ta nesanci yin wani abu wanda zai jefa yankin cikin yakin da ba a san yadda karshensa zai kare ba. Haka nan kuma ya ce; Tushen matsalar tana nan a cikin kasar India,kuma wadanda su ka shirya kai harin suna nan a cikin India, don haka a cikin India ya kamata ta neme su.”
A lokaci daya kuma ministan tsaron na Pakistan ya jadada cewa; Kasarsa ba ta da sha’awar yaki ko kadan, amma idan aka kallafa mata yaki, to martanin da za ta mayar zai zama mafi dacewa kuma cikin karfi.”
A nashi gefen, ministan harkokin wajen kasar Pakistan Muhammad Ishaq Dar, ya ce, kasarsa tana sa ido da bibiyar abinda India take yi a kusa, kuma a shirye take ta kare tsaronta da iyakokinta.”
Dar ya kuma fada wa wata tashar talabijin din cewa; Pakistan kasa ce da take da makaman Nukiliya, tana kuma da dandazon makamai masu linzami masu karfi, kuma India ta kwana da sanin hakan, don haka ta guji keta hurumin kasar Pakistan da tsaronta.”
India ta zargi Pakistan da hannu a harin da aka kai a yankin Kashmir wanda ya yi sanadiyyar mutane 26. Kasar ta India ta kori Jakadan Pakistan daga kasarta, sannan kuma ta kira yi nata jakadan daga Islamabad. Bugu da kari Indiyan ta dakatar da aiki da yarjejeniya akan ruwa a tsakanin kasashen biyu.