Kasar Rasha ta ce Janye tallafin Soji da Amurka take bawa Ukrain zai kawo zaman lafiya.
Published: 4th, March 2025 GMT
A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji
Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce: ya kamata mu yi dubi kan lamarin, “Idan har da gaske ne, to wannan shi ne mataki da zai sanya Kyiv ta nemi cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
Peskov ya kara da cewa Da ma Amurka ce ke sahun gaba wajen samar wa da Ukraine makamai. “Don haka idan ta daina ko ta dakatar da bai wa Ukraine agajin soji, to shi ne abin da yafi dacewa kuma shi ne zai kawo zaman lafiya,” a cewarsa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Malaman Musulmi ta yi kira da a dakatar da kisan kiyashi a Gaza cikin gaggawa
Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka.
A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman musulmi ta duniya ta yi kira ga duniya da ta bayyana goyon bayanta ga al’ummar Palasdinu ta hanyar daukar matakan gaggawa da suka hada da dukkanin hanyoyin soja, tattalin arziki, da diflomasiyya mai inganci.
Dangane da haka ne kungiyar ta yi kira ga limaman masallatan Juma’a a fadin duniya da su sadaukar da hudubar sallar Juma’a na gobe don magana kan wajabcin magance wahalhalu da radadin al’ummar Palastinu da kuma bukatar kawo karshen kisan gillar da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa Palastinawa.
Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta jaddada a cikin wannan bayani cewa, wannan cibiyar ta bibiyi matukar damuwa da bakin ciki da kisan gilla, da laifukan yaki , da yunwa da kishirwa, da kuma gudun hijira da gwamnatin yahudawan sahyoniya tare da goyon bayan ma’abota girman kan duniya suka saka mazauna Gaza a ciki.
Kungiyar ta kuma yi kira ga kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama da su ci gaba da tallafawa Gaza da kuma tattara laifukan da ake aikatawa har sai an dakatar da harin, da kuma tabbatar da adalci. Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta kuma yi kira da a gudanar da jerin gwano na lumana bayan sallar Juma’a a gobe a dukkanin kasashen musulmi, domin bayyana goyon bayansu ga zirin Gaza da kuma yin Allawadai da ayyukan wuce gona da irin Isra’ila.